Dillalai Sun Fadi Sakamakon da Tattaunawa da Matatar Dangote Za Ta Haifar

Dillalai Sun Fadi Sakamakon da Tattaunawa da Matatar Dangote Za Ta Haifar

  • Yayin da majalisar wakilan kasar nan ke fafutukar gwamnati ta rage farashin fetur, kungiyar IPMAN ta ce sauki na tafe
  • Kungiyar dillalan fetur ta kasa (IPMAN) ta ce ganawar da ta ke yi da matatar Dangote zai haifar da da mai ido kan farashin
  • Shugaban kungiyar, Abubakar Shettima ya kara da cewa kamfanin NNPCL zai fara loda feturin da 'yan IPMAN suka saya a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Kungiyar dillalan fetur ta kasa (IPMAN) ta shaidawa yan kasar nan cewa tattaunawa ta yi nisa tsakaninta da matatar Dangote.

Shugaban kungiyar, Abubakar Shettima ne ya tabbatar da haka a ranar Laraba yayin kaddamar da kwamitin sanya idanu kan masu satar fetur da lalata butun mai a Fatakwal.

Kara karanta wannan

"Za a samu matsala:" Majalisa ta hango barazanar tashin hankali kan tsadar fetur

Fetur
IPMAN ta kara albishir da yiwuwar saukar farashin fetur Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Jaridar Leadership ta kara da cewa ana sa ran zaman da IPMAN ke yi da matatar Dangote za ta haifar da da mai ido ta hanyar rage farashin man fetur a kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dillalan mai sun farashin fetur zai ragu

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa kungiyar IPMAN ta bayar da tabbacin za a iya samun ragi a kan yadda ake sayen litar fetur a yanzu.

Abubakar Shettima ya ce farashin zai sauko ne saboda Darakta janar na hukumar tsaron DSS, Kayode Ajayi ya shiga tsakanin dambarwarsu da NNPCL.

IPMAN: NNPCL zai fara lodawa dillali fetur

Kan batun neman kamfanin NNPCL ya dawo masa da kudin fetur da aka hana kungiyar IPMAN., shugaban kungiyar Abubakar Shettima ya ce ana tattaunawa da kamfanin.

Ya ce kamfanin NNPCL ya dauki alkawarin za a fara loda fetur domin kai wa ga 'ya'yan kungiyar IPMAN da zummar su fara sayarwa jama'ar kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan rasa rayuka a Jigawa, barci ya dauke direba, wata tankar fetur ta kama da wuta

Majalisa ta shiga batun tsadar man fetur

A wani labarin kun ji cewa majalisar wakilai ta tsoma bakinta cikin lamarin karuwar farashin man fetur, inda a yanzu NNPCL ke sayar da kowace lita a kan sama da N1,000.

Majalisar ta shaidawa gwamnatin tarayya akwai barazana ga zaman lafiya a kasar nan bayan karin da aka yi na baya-bayan nan, wanda shi ne karo na hudu a kasa da shekaru biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.