Hukumar Kwastam: Yadda Aka Kama Tulin Makaman N9.5bn Za a Shigo da Su Najeriya

Hukumar Kwastam: Yadda Aka Kama Tulin Makaman N9.5bn Za a Shigo da Su Najeriya

  • Hukumar kwastam ta fitar da rahoto kan makaman da ta kama ana shirin shigowa da su Najeriya a tsawon shekaru shida
  • Shugaban hukumar kwastam, Adewale Adeniyi ne ya fitar da rahoton yayin wani taron da suka bayyana nasarorin da suka samu
  • Ana zargin ana shirin shigo da makaman ne domin yan bindiga irinsu Bello Turji da sauran miyagun da suka addabi bayin Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar kwastam ta fitar da rahoto kan nasarorin da ta samu wajen kama makamai da ake shirin shigowa da su Najeriya.

Daga shekarar 2018 zuwa yau, kwastam ta kama tulin makamai da suka kai kusan Naira biliyan 10.

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyya: An bayyana lokacin da Damagum zai sauka daga shugaban PDP

Kwastam
Kwastam ta kama makaman kusan N10bn. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kwastam, Adewale Adeniyi ne ya fitar da rahoton yayin wani taro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makaman da kwastam ta kama a Najeriya

Shugaban kwastam, Adewale Adeniyi ya bayyana cewa sun kama makamai da kimarsu ta kai N9.58bn daga 2018 zuwa yau da ake shirin shigowa da su Najeriya.

Adewale Adeniyi ya bayyana cewa sun kama makamai mabanbanta da suka kai 10,498 da tarin harsashi da suka kai 114,929 a tsawon shekarun.

Makaman da aka kama a shekara 1 a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumar kwastam ta bayyana cewa ta kama kashi 60% na makaman ne a cikin shekara daya da ta wuce.

A cikin shekara daya da ta wuce yan ta'adda irinsu Bello Turji sun yawaita kai hare hare kan al'umma da garuruwa a Arewacin Najeriya.

Hukumar Kwastam za ta cigaba da ƙoƙari

Kara karanta wannan

Daidaiton jinsi: Tinubu ya bayyana babban kudurin gwamnatinsa kan matan Najeriya

Shugaban hukumar kwastam ya bayyana cewa kama makaman na cikin kokarin da suke yi wajen ba da tsaro a iyakokin Najeriya.

Adewale Adeniyi ya kara da cewa lamarin na tono irin dabarun da masu shigo da kaya ta barauniyar hanya ke yi zuwa Najeriya.

Kwastam ta karya farashin man fetur

A wani labarin, Legit ta ruwaito cewa hukumar kwastam ta karya farashin man fetur a jihar Adamawa da ke Arewacin Najeriya.

Hukumar kwastam ta karya farashin ne a wasu gidajen mai guda biyu a jihar, ta rika sayar da man fetur a farashi mai rahusa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng