Gwamnatin Tinubu da Ƴan Kwadago Sun Cimma Matsaya kan Farashin Kayan Abinci
- Gwamnatin tarayya ta amince da matakan rage tsadar sufuri da kayan abinci a zamanta da ƴan kwadago a ranar Laraba
- Rahotanni sun nuna cewa gwamnati za ta kara fito da motocin bas na CNG wanda za su taimaka wajen karya farashin abinci
- A ƴan watannin nan dai ƴan Najeriya na fama da hauhawarar farashin muhimman kayayyakin amfaninsu na yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun cimma matsaya kan hanyoyin da za a bi wajen ragewa ƴan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa.
A zaman da suka yi jiya Laraba, 16 ga watan Oktoba, ɓangarorin biyu sun fahimci juna kuma sun amince da hanyoyin rage tsadar sufuri da kayayyakin abinci.
Majalisa ta nemi a rage farashin man fetur
Vanguard ta tattaro cewa wannan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar tarayya ta buƙaci gwamnati ta soke ƙarin farashin fetur da aka yi kwanan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar ta kuma buƙaci gwamnati ta gagauta ɗaukar matakan saita farashin fetur da na iskar gas na girki domin. sauƙaƙawa ƴan Najeriya.
Sai dai a zaman da suka yi a ofishin sakataren gwamnatin tarayya jiya Laraba da daddare, gwamnati ta faɗawa ƴan kwadago matakan da za ta ɗauka.
Gwamnatin Tinubu za ta zauna da gwamnoni
Daga ciki gwamnati ta ce za ta kira taron gwamnonin jihohi domin tabbatar da kowanensu ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Wasu majiyoyi da suka halarci zaman sun shaida cewa gwamnati da ƴan kwadago sun amince za su ci gaba da zaman tattaunawa a kai-a-kai domin dawo da dangantakarsu ta baya.
Wasu matakan da gwamnati ta shirya ɗauka
Wata majiya ta ce:
"Da farko gwamnati ta yarda za ta saki na'urorin canza ababen hawa daga amfani da fetur zuwa gas watau CNG, sannan ta amince za ta kara ba NLC motocin bas 45 masu amfani da gas, 90 kenan jimulla.
"A kokarin karya tsadar sufuri, gwamnatin tarayya ta amince za ta zauna da gwamnoni ta nuna masu amfanin motocin bas masu amfani da gas watau CNG.
"Hakan kuma zai rage farashin kayayyakin abinci domin za a samu saukin kuɗin safarar kaya daga ɓangarori daban-daban a ƙasar nan."
Gwamnatin ta kuma yi alkawarin gaggauta kammala aikin matatun mai domin karya farashin fetur, inda ta ce matatu biyar na dab da fara aiki, rahoton Channels tv.
TUC ta bukaci Tinubu ya sauke farashin mai
A wani labarin kuma ƙungiyar ‘yan kwadago ta TUC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da farashin fetur kamar yadda yake a Yunin 2023.
A wani taron manema labarai a Abuja, kungiyar TUC ta ce ba wai iya mayar da fetur farashin shekarar 2023 ba, ana so ya yi kasa da haka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng