'Kun Kauce', Malamin Izalah ya Soki Wasu Malaman Sunnah da Suka Koma Neman Mabiya

'Kun Kauce', Malamin Izalah ya Soki Wasu Malaman Sunnah da Suka Koma Neman Mabiya

  • Malamin addinin Musulunci ya soki yadda wasu malaman sunnah suka sauya salon koyarwa yadda ya dace
  • Sheikh Aliyu Muh'd Sani ya nuna damuwa kan yadda ake yin wa'azi yau domin neman mabiya a kafofin sadarwa
  • Shehin ya kawo misalai da yadda marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud da Sheikh Kabiru Gombe suke karantarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bauchi - Malamin Musulunci, Sheikh Aliyu Muh'd Sani ya yi magana kan salon koyarwar malaman addini a yanzu.

Malamin ya koka kan yadda malaman Sunnah suka kauce hanyar koyarwar da ta dace, sun shiga neman mabiya a shafukan sadarwa.

Malamin Izalah ya soki tsarin wasu malaman sunnah
Sheikh Aliyu Muh'd Sani ya koka kan yadda malaman sunnah suka sauya salon koyarwa. Hoto: Zainab Ja'afar Mahmud, Aliyu Muh'd Sani.
Asali: Facebook

Malamin Musulunci ya soki wasu malaman sunnah

Sheikh Aliyu ya bayyana haka a cikin wata sanarwar jan hankali da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

T-Pain da sauran sunaye 4 da aka lakawa Tinubu da dalilan alakanta shi da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce malaman Sunnah sun kauce hanyar jan kunne kan shirka da bidi'o'i inda suka koma wa'azin mata da bakwanci.

Shehin ya ba da misalin yadda Sheikh Kabir Haruna Gombe da marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ke karantarwa yadda ya dace.

"A baya Malaman Sunnah suna samun shahara ne saboda matsawa a kan kira ga Tauhidi da Sunna, da raddi ga masu shirka da bidi'o'i, Shiyasa mutane da dama ke jin haushin Malam Kabir Gombe, da ire-irensa kamar Malam Ja'afar Mahmud Adam."
"Abin takaici, a yau Malamai suna samun shahara ne da wa'azozin mata da na ma'aurata, a ciki har da fadin abubuwan da ba su dace ba a bainar jama'a."
"Wasu kuma sun shahara da yawan ba da labaru alhali idan aka yi bincike labarin bai tabbata ba, wasu sun zama 'yan barkwanci da ba da dariya ga 'yan mata da samari."

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci a Kano sun haɗa kai, sun aika saƙo ga mutanen jihar Borno

- Sheikh Aliyu Muh'd Sani

An yi watsi da malaman kwarai a yau

Malamin ya ce abin takaici ne wadanda ke koyarwa hanyar da ya dace ba su samun hankulan mafi yawan mutane saboda ba wancan layin suke bi ba.

Ya shawarci malamai su kara kaimi wurin jan hankalin al'umma kan abubuwan da suka dace duk da tabbas ya sani ana kokari sosai.

Sheikh Salihu Zaria ya magantu kan Muslim/Muslim

Kun ji cewa Malam Salihu Abubakar Zaria ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar zaben Bola Tinubu a tsarin Musulmi da Musulmi ba.

Sheikh Salihu ya ce ko kadan ba tsarin Musulmi da Musulmi ba ne ya kawo damuwar da ake ciki, ya ce lamarin daga Allah SWT ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.