Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Yadda za Ta Raba Yan Najeriya Miliyan 100 da Talauci

Gwamnatin Tarayya Ta Fadi Yadda za Ta Raba Yan Najeriya Miliyan 100 da Talauci

  • Gwamnatin tarayya ta ce jama'a su kwantar da hankalinsu domin ana kokarin fitar da yan kasar nan daga kangin talauci
  • Ministar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ya bada tabbacin, ya ce za a cimma matakin nan da 2030
  • Ya ce akwai hanyoyi daban daban da gwamnati ke bi wajen tabbatar da cewa an raba akalla mutane miliyan 100 da fatara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ce a cikin wasu shekaru, za ta fitar da jama'ar kasar nan akalla miliyan 100 daga kangin talauci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta yi bincike kan mutuwar mutane sama da 100 a Jigawa

Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka, ya ce akwai wasu shirye-shirye da aka fitar domin cimma manufar kafin 2030.

Fetur
Gwamnati na shirin fitar da mutane miliyan 100 daga talauci Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Ministan Tinubu ya bayar da tabbacin a taron masu ruwa da tsaki kan amfani da ruwa wajen noman rani da ya gudana a Uyo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakan gwamnati wajen raba jama'a da talauci

Gwamnatin tarayya ta bayyana wasu daga cikin hanyoyin da ta ke bi wajen tabbatar da daga likkafar yan kasar nan miliyan 100 daga talauci.

Daga cikin tsare-tsaren da Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Farfesa Joseph Utsev ya ce ana dauka akwai inganta noman rani da na damina.

Gwamnati na shirin cirewa mutane rigar talauci

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ce a shirye ta ke ta rungumi tsarin gwamnatin tarayya na tabbatar da an raba yan kasar nan da kangin rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kadu da faduwar tankar fetur a Jigawa, an fadi matakin da za a dauka

Gwamna Umo Eno, wanda mataimakinsa Sanata Akon Eyakenyi ya wakilta ya bayyana cewa za ta magance matsalar rashin abinci da ake fuskanta a fadin jihar.

Kwamitin gwamnati ya gano dalilin talauci

A wani labarin, mun ruwaito cewa kwamitin gwamnatin tarayya kan tsare-tsare da yi wa harkokin haraji garambawul ya ce zurarewa da kudin shigar kasa ke yi matsala ce babba.

Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa idan aka magance zurarewar kudin gwamnatin, Najeriya kasa ca mai arzikin da za ta rike kanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.