Tsadar Fetur: Ministan Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Daina Korafi

Tsadar Fetur: Ministan Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Daina Korafi

  • Ministan makamashi na Najeriya, Adebayo Adelabu ya yi nuni da cewa an samu wadatar wutar lantarki a ƙasar nan
  • Adelabu ya nuna cewa hakan ne ya sa ƴan Najeriya suka daina ƙorafi kan tsadar fetur saboda ba su buƙatar janaretoci
  • Ya ce da a ce sai an siya fetur da tsada a kafin a samu lantarki, da surutun da ƴan Najeriya za su yi, ya fi wanda suke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana dalilin da ya sa ƴan Najeriya suka daina ƙorafi a kan tsadar man fetur.

Adebayo Adelabu ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun daina ƙorafi kan tsadar fetur ne saboda a yanzu ba su dogara da janaretocinsu ba kafin su samu lantarki.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur na iya sauka yayin da Majalisa ta sa baki kan ƙarin da aka yi

Adelabu ya ce an daina korafi kan tsadar lantarki
Adebayo Adelabu ya nuna cewa lantarki ta wadata a Najeriya Hoto: Hon. Adebayo Adelabu
Asali: Twitter

NNPCL ya ƙara kuɗin man fetur

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron baje kolin makamashi na Najeriya na shekarar 2024 a Legas, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata, farashin litar man fetur ya tashi zuwa N998 da N1,030 da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyarsa da matatar man Dangote. 

Minista ya ce wutar lantarki ta wadata

Sai dai, da yake jawabi a wajen taron, ministan ya ce mutane ba su yin hayaniya game da ƙarin kuɗin saboda ba sai sun sayi man fetur a kan Naira 1000 domin sanyawa a janaretocinsu kafin su samu wutar lantarki ba.

A cewar Adelabu, gwamnatin tarayya ta ƙudiri aniyar maye gurbin dukkanin janaretoci a ƙasar nan kamar irin shirin jihar Legas na sauya janaretoci miliyan ɗaya a cikin shekara guda, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar da haka.

Kara karanta wannan

Farashin fetur: NNPCL ya musanta cimma yarjejeniya da IPMAN, ya bayyana yadda abin yake

"Mutane ba sa buƙatar siyan mai kamar yadda suke yi a baya domin samun wutar lantarki. Shi ya sa surutun bai yi yawa ba sosai."
"Idan da za a ce sai sun je gidajen mai sun sayi fetur a kan N1000 kan kowace lita domin samun wutar lantarki, da surutun da mutane za su riƙa yi da yafi na yanzu."

- Adebayo Adelabu

An buƙaci Tinubu ya kori minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar marubutan kare hakkokin dan Adam ta Najeriya (HURIWA) ta bukaci Bola Tinubu da ya gaggauta korar ministan makamashi, Adebayo Adelabu.

HURIWA ta nuna rashin gamsuwa da kuma bacin ranta dangane da yawan lalacewar babbar tashar wutar lantarki ta kasa a karkashin gwamnatin Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng