"Allah Ji ƙansu," Gwamnan Abba Ya Yi Maganar Mutuwar Sama da Mutum 100 a Jigawa
- Gwamnan Kano ya yi ta'aziyyar mutanen da suka rasu sakamakon gobarar da ta tashi daga fashewar tankar mai a jihar Jigawa
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana rashin da aka yi a matsayin wanda ya shafi ƙasa baki ɗaya, inda ya yi addu'ar Allah ya ji ƙansu
- Mutane sama da 100 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu akalla 70 suka jikkata sakamakon fashewar tankar fetur a garin Majiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika saƙon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jigawa bisa ibtila'in fashewar tankar mai wanda ya yi ajalin mutane sama da 100.
Gwamna Abba ya bayyana lamarin da ya laƙume rayukan mutane sama da 100 tare da jikkata wasu da dama a matsayin babban abin takaici da ya shafi ƙasa baki ɗaya.
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda tanka ta kashe mutane a Jigawa
Idan ba ku manta ba mun kawo maku rahoton yadda wata tanka maƙare da fetur ta fashe a garin Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Fashewar tankar ya tada mummunar gobara da ta zama ajalin mutane kusan 150 kawo yanzu, wasu akalla 70 na kwance ana yi masu magani a asibiti.
Gwamnatin Kano ta miƙa sakon ta'aziyya
Da yake miƙa sakon ta'aziyya ga waɗanda lamarin ya shafa, Gwamna Abba ya yi addu'ar Allah ya ji ƙan waɗanda suka rasu kuma ya ba waɗanda suka ji rauni lafiya.
"Mun samu labarin wata mummunar gobara da ta afku a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a Jigawa, wanda ya yi sanadin asarar rayuka tare da kwantar da wasu da dama a asibiti.
“A madadin gwamnati da jama’ar Kano, ina mika sakon ta’aziyya ga Gwamna Umar Namadi, gwamnati da al'ummar Jigawa, musamman iyalan wadanda suka rasu da mutanen garin Majiya."
- Abba Kabir Yusuf.
Gwamnati za ta binciki fashewar tanka a Jigawa
A wani labarin kuma gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan mummunan hadarin motar mai da ya laƙume rayuka da dama a jihar Jigawa.
Karamin Ministan harkokin man fetur ya bayyana cewa ba za a bar abin ya tafi a banza ba, za a binciko sababbin faruwar mummunan haɗarin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng