Gwamna Ya Kafa Tarihi, Zai Biya Mafi Ƙarancn Albashin N100,000, Ya Fadi Dalilai
- Yayin da kowane gwamna ke fadin abin da zai biya, gwamnatin jihar Lagos ta ciri tuta kan biyan mafi ƙarancin albashi
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya amince da biyan N85,000 ga ma'aikatan jiharsa duba da tsadar rayuwa da ke addabarsu
- Sanwo-Olu ya ce zuwa watan Janairun 2025, zai so ya kara mafi ƙarancin albashin ma'aikata zuwa N100,000 a duk wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos ya yi magana kan sabon albashin N70,000.
Gwamna Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa ta shirya biyan ma'aikata N85,000 duba da halin da ake ciki.
Gwamna Sanwo-Olu ya shirya biyan albashin N100,000
Gwamnan ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da Channels TV ta wallafa a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanwo-Olu ya sha alwashin kara mafi ƙarancin albashi har N100,000 zuwa watan Janairun 2025 da ke tafe.
Ya nuna ba wai ya fadi haka ne domin gasa da sauran gwamnoni ba, ya ce ya duba yanayin rayuwar jihar Lagos ne.
"Zan so dawowa nan a watan Janairun 2025 na ce maka na kara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan jihar Lagos zuwa N100,000."
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu
Legit Hausa ta tattauna da wani ma'aikaci
Wani ma'aikaci a gwamnatin jihar Gombe ya yi tsokaci kan matakin gwamnan Lagos na biyan mafi ƙarancin albashi.
Sadiq Abdulkadir ya ce gwamnan ya ciri tuta duba da yanayin tsadar rayuwa musamman a jihar Lagos.
Sai dai ya ce ko ina akwai tsadar rayuwa amma dole a yabawa gwamnan saboda yafi sauran gwamnoni.
Sadiq ya kuma yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan amincewa da biyan N71,450 na mafi ƙarancin albashi inda ya soki masu korafi kan haka.
Karanta sauran labarai kan mafi ƙarancin albashi
- Gwamna Zulum Ya Amince da Sabon Mafi Karancin Albashi, Ya Sa Lokacin Fara Biya
- Ta Leko Ta Koma: Gwamna Ya Musanta Amincewa da Mafi Karancin Albashin N70,000
- Gwamna Ya Faranta Ran Ma'aikata, Zai Biya N73,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi
Gwamnan Delta ya umarci biyan sabon albashi
Kun ji cewa Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta ya umarci fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ƙananan ma'aikata.
Gwamna Sheriff ya ba da umarnin biyan ne nan take wanda za a fara ba ma'aikata a karshen watan Oktoban 2024 da muke ciki.
Sakataren gwamnatin jihar ya tabbatar da haka, ya ce gwamnan ya duba halin da al'umma ke ciki ne na tsadar rayuwa a yau.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng