Ba a Gama Rikicin Masarautar Kano ba, Sanusi II Ya Sake Nadin Sarauta a Jihar

Ba a Gama Rikicin Masarautar Kano ba, Sanusi II Ya Sake Nadin Sarauta a Jihar

  • Ana cigaba da rikicin masarauta a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya sake nadin sabuwar sarauta a jihar
  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya amince da nadin Alhaji Gambo a matsayin Jakadan Garko da ke jihar Kano
  • Rahotanni sun ruwaito cewa za a gudanar da bikin nadin sarautar da yammacin yau Laraba 17 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya sake amincewa da nadi a masarautarsa.

Muhammadu Sanusi II ya amince da nadin Alhaji Gambo a matsayin Jakadan Garko a jihar Kano.

Sarki Sanusi II ya nada Jakadan Garko a Kano
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Alhaji Gambo a matsayin Jakadan Garko. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Nadin sarauta da Sanusi II ya yi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ta wallafa a shafin X a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Yadda Abba ya kashe wata wutar rikicin da aka kunna masa a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Muhammadu Sanusi II ya amince da yin nadin Abba Yusuf wanda kawu ne ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin Dan Makwayon Kano.

Sanusi II ya zabi Abba Yusuf daga gidan Galadiman Kano ya zama Dan makwayon Kano wanda za a nada shi ranar 18 ga watan Oktoban 2024 da muke ciki.

Yaushe za a yi nadin sarautar a Kano?

Sanarwar ta ce Sarki Muhammadu Sanusi II ya sahale da nadin Shamakin Garko domin inganta masarautarsa.

Za a gudanar da nadin sarautar da yammacin yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024 a masarautar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a gudanar da nadin ne da yammaci a kofar Kwaru gidan Sarkin Kano.

Kotu za ta saurari shari'ar masarautar Kano

Kun ji cewa Kotun Daukaka Kara za ta fara zaman sauraron kararrakin da aka shigar gabanta kan rigimar sarautar Kano a ranar 17 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Rikicin sarautar Kano ya dawo, kotun ɗaukaka ƙara ta yi magana

Wannan dai na zuwa ne yayin da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammadu Sanusi II ke cigaba da nuna kansu a matsayin sarakuna a jihar.

An fara rigima kan sarautar Kano ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rusa masaurautu biyar kuma ya dawo da Muhammadu Sanusi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.