Ana Kewar Rashin Tinubu, Shettima Zai Shilla Ketare, An Samu Bayanin Tafiyar
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai tafi Sweden domin wakiltar Najeriya kan wasu muhimman abubuwa
- Kashim Shettima zai ziyarci kasar Sweden domin tattaunawa kan wasu lamura masu muhimmanci saboda a kawo sauyi
- Wannan na zuwa yayin da ake dakon dawowar Bola Tinubu da ke Faransa bayan barin Burtaniya a cikin kwanakin nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai tsallaka zuwa kasar Sweden.
Shettima zai tafi Sweden domin ziyarar kwanaki biyu kan wasu yarjejeniya a tsakanin kasashen guda biyu.
Kashim Shettima zai shilla Sweden na kwana 2
NTA News ta wallafa hakan a shafinta na X cewa Shettima zai kai ziyarar domin kawo abubuwan cigaba ga kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Shettima a bangaren sadarwa, Stanley Nkwocha ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024.
Nkwocha ya ce Shettima zai kai ziyarar domin wakiltar Bola Tinubu game da alaka tsakanin kasashen guda biyu.
Musabbabin ziyarar Shettima a kasar Sweden
"Kashim Shettima zai tattauna kan lamuran da suka shafi sadarwa ta zamani da ilimi da harkokin noma da kuma al'adu."
"Sauran sun hada da bangaren Sufuri da hakar ma'adinai da kuma sauran harkokin cigaba ma zamani da za su kawo sauyi."
"Mataimakin shugaban kasar zai gana da masu ruwa da tsaki a ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu."
- Stanley Nkwocha
Hakan na zuwa ne yayin da yan Najeriya ke dakon Shugaba Bola Tinubu da ke cigaba da hutun makwanni biyu a kasar Faransa bayan barin kasar Burtaniya.
An bukaci kasafin kudi daga Tinubu
Kun ji cewa an ruwaito Majalisar Wakilai ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kasafin kudin shekarar 2025 mai kamawa.
Majalisar ta bukaci Bola Tinubu ya gabatar mata da kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba domin ta samu damar yin bahasi a kansa.
A yanzu haka dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutun mako biyu ƙasar Birtaniya, daga can kuma ya wuce kasar Faransa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng