Farashin Man Fetur Na Iya Sauka yayin da Majalisa Ta Sa Baki kan Ƙarin da Aka Yi

Farashin Man Fetur Na Iya Sauka yayin da Majalisa Ta Sa Baki kan Ƙarin da Aka Yi

  • Mai yiuwa a samu saukin tsadar man fetur da majalisar wakilan tarayya ta sa baki kan ƙarin farashin lita a Najeriya
  • A zamanta na ranar Laraba, majalisar ta buƙaci a gaggauta soke ƙarin farashin da aka yi kwanan nan saboda ya kara jefa mutane cikin wahala
  • Tun bayan cire tallafin mai ranar 29 ga watan Mayu, 2024, ƴan Najeriya suka fara fuskantar tsadar man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da rayuwa ke ƙara tsada a ƙasar nan, majalisar wakilan tarayya ta tsoma baki kan ƙarin farashin man fetur a Najeriya.

Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta soke ƙarin farashin man fetur da gas na girki domin saukaƙawa mutane halin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Mutane kusan 100 sun rasu sakamakon fashewar tankar mai a Jigawa

Majalisar wakilai.
Majalisa ta bukaci a soke ƙarin farashin man fetur da gas na girki a Najeriya Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Channels tv ta ce majalisar wakilai ta ɗauki wannan mataki ne a wani kudiri da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Aliyu Madaki da ƴan majalisa 111 suka gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta nuna damuwa da karin

Ƴan majalisar sun koka cewa karin farashin fetur da gas na ƙara tunkuɗa ƴan Najeriya cikin wahala kuma barazana ce ga sana'o'i da dama.

Hakan ya sa majalisar wakilai ta umarci kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL da ma'aikatar man fetur su lalubi hanyoyin da za a kara yawan man da ake tacewa a gida domin ya yi arha.

Bugu da ƙari majalisar ta bukaci babban bankin Najeriya watau CBN ya ɓullo da tsare-tsaren da suka dace domin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki bayan tashin mai.

Yadda fetur ya tashi bayan hawan Tinubu

Tun bayan tuge tallafun man fetur da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi, farashin litar mai ta ci gaba da tashi a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisar PDP sun rasa kujerunsu, an ba INEC damar shirya sabon zaɓe

Fetur ya kara tsada daga kusan N200 sai da kowace lita ɗaya ta haura N1,000, hakan ya sa farashin kayayyaki ya kara hauhawa, cewar Leadership.

Sai dai majalisar wakilai ta nuna damuwa kan halin da mutane za su shiga musamman bayan ƙarin da aka yi kwanan nan, ta umarci a soke sabon ƙarin.

NNPCL da ƴan kasuwa sun daidaita

A wani rahoton kuma kamfanin NNPCL da kungiyar yan kasuwar man fetur sun cimma matsaya kan farashin litar mai.

Rahotanni sun nuna cewa an samu daidaiton ne bayan shiga tsakani da hukumar tsaron farin kaya watau DSS ta yi kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262