Gwamnati Ta Kadu da Faduwar Tankar Fetur a Jigawa, An Fadi Matakin da Za a Dauka
- Gwamnatin tarayya ta bayyana kaduwarta bisa asarar rayuka sama da 100 a gobarar tankar fetur da ya afku a jihar Jigawa
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya mika ta’aziyya ga gwamnati da jama’ar jihar, inda ya ce gwamnati za ta taimaka
- Mutane akalla 107 ne su ka riga mu gidan gaskia, yayin da wasu adadinsu ke kwance a asibitin su na samun kulawar likitoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Gwamnatin tarayya ta shiga alhinin asarar rayuka bayan fashewar tankar fetur da ta salwantar da rayuka akalla 107 a Jigawa.
A daren Talata ne wata mota makare da man fetur ta kife a Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, daga bisani jama’a su ka zo diba.
A sakon da hadimin ofishin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, ya ce gwamnati ba ta ji dadin asarar rayuka da aka samu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati za ta tallafawa mutanen Jigawa
NTA News ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tallafawa mutanen da gobarar tankar fetur ta shafa ta dukkanin hanyoyin da su ka dace.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana haka a madadin shugaba Bola Tinubu, tare da mika ta’aziyya ga gwamntin jihar Jigawa ga iyalan wadanda iftila’in ya shafa.
Gwamnati za ta duba matakan safarar fetur
Gwamnatin Bola Tinubu ta bukaci a fara duba kan dukkanin matakan da ake bi wajen safarar man fetur domin kare makamancin mummunan hadarin tankar Jigawa.
Mataimakin shugaban kasar nan, Kashim Shettima ya ce asarar rayuka da hadarin ya jawo babban iftila’i ne, tare da addu’ar Allah Ya sada mamatan da rahamarsa.
Tankar fetur ta fadi a Jigawa
A wani labarin kun ji cewa wata tankar fetur ta fadi a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, inda ta jawo asarar rayuka sama da 107, yayin da wasu ke kwance a asibitin.
Rundunar yan sandan Jigawa ta bayyana cewa sai da ta yi kokarin jama’a zuwa wurin da tankar ta fadi, amma ajali ya riga ya kira mutane da dama, kuma tuni aka birne su da ranar yau Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng