Tsadar Fetur: Kungiyoyin Kwadago Sun Sa Labule da Gwamnati, An Samu Bayanai

Tsadar Fetur: Kungiyoyin Kwadago Sun Sa Labule da Gwamnati, An Samu Bayanai

  • Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC sun shiga ganawa da gwamnatin tarayya kan halin da ake ciki
  • Shugabannin ƴan ƙwadagon suna ganawa da gwamnatin tarayyar ne kan ƙarin farashin man fetur da kamfanin NNPCL ya yi
  • Ana yin ganawar ne tare da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da wasu jiga-jigan gwamnati a birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugabannin ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), da takwarorinsu na TUC, na ganawa da gwamnatin tarayya.

Shugabannin na ƙungiyoyin ƙwadagon sun shiga ganawa da gwamnatin tarayyar ne a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoban 2024.

Kungiyoyin kwadago sun sa labule da gwamnatin tarayya
NLC da TUC sun sa labule da gwamnatin tarayya Hoto: @DOlusegun, @NLCheadquarters
Asali: Facebook

Ƴan ƙwadago sun gana da gwamnati

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa taron ya ta’allaƙa ne kan halin da ƙasa nan ke ciki, musamman tashin farashin man fetur da yadda hakan ya shafi ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Farashin fetur: NNPCL ya musanta cimma yarjejeniya da IPMAN, ya bayyana yadda abin yake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron dai na gudana ne tare da sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.

A wajen taron akwai mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ƙaramar ministar ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha da ministan kuɗi Wale Edun.

Sauran sun haɗa da ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, ƙaramin ministan fetur, Heineken Lokpobiri, ƙaramin ministan albarkatun iskar gas Emperikpe Ekpo da wakilan kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL).

Ganawar na zuwa ne yayin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ke ci gaba da hutunsa a ƙasar waje.

Karanta wasu labaran ƴan ƙwadago

Kara karanta wannan

Jagororin APC sun ba 'yan Najeriya shawara kan gwamnatin Tinubu

Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnati shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar kwadago ta TUC ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta dawo da farashin fetur kamar yadda yake a watan Yunin 2023.

Shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo ya ce ba wai suna neman a mayar da farashin man yadda yake a baya kadai ba, suna so ne farashin ya sauka kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng