DSS Ta Mamaye Majalisa da Zargin Shirin Tsige Akpabio? An Samu Bayanai

DSS Ta Mamaye Majalisa da Zargin Shirin Tsige Akpabio? An Samu Bayanai

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya musanta labarin cewa an yi yunkurin tsige shi daga mukaminsa
  • Akpabio ya kuma karyata cewa jami'an hukumar DSS sun dira a dakin Majalisar domin hana shirin tsige shi da ake yi
  • Hakan ya biyo bayan yada wasu rahotanni da ke cewa ana shirin tsige Akpabio daga mukaminsa a yau Laraba a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi magana kan zargin shirin tsige shi da ake yi a birnin Abuja.

Godswill Akpabio ya karyata rahoton da ake yadawa, ya ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya kan lamarin da ake yadawa.

Akpabio ya mayar da martani kan zargin shirin tsige shi da ake yi
Shugaban Majalisar Tarayya, Godswill Akpabio ya karyata yunkurin tsige shi. Hoto: Godswill Obot Akpabio.
Asali: Facebook

Akpabio ya musanta yunkurin tsige shi

Kara karanta wannan

Rikicin jam'iyya: An bayyana lokacin da Damagum zai sauka daga shugaban PDP

Shugaban Majalisar ya fadi haka ne yayin zamansu a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024 a Abuja, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpabio ya kuma karyata cewa jami'an DSS sun mamaye Majalisar domin dakile shirin tsige shi da ake yi.

Shugaban Majalisar ya ce watakila masu yada labarin na neman kudi ne saboda magoya baya da za su samu kan lamarin.

Akpabio ya bukaci yin bincike kan jita-jitar

"Sun ce wai jami'an DSS sun mamaye Majalisar Dattawa saboda dakile yunkurin tsige shugabannin Majalisar."
'Babu yadda za ka dakile yaduwar kafofin sadarwa, muna zaune a nan muna yin aikinmu cikin aminci ba tare da matsala ba."
"Yanzu wani kwamiti za mu tura wannan lamarin domin su yi bincike.{Dariya}"

- Godswill Akpabio

Akpabio ya mika bukata ga kwamitin ayyuka na musamman domin yin bincike da dawo da rahoto cikin gaggawa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Daidaiton jinsi: Tinubu ya bayyana babban kudurin gwamnatinsa kan matan Najeriya

Halin kunci: Akpabio ya sha suka kan kalamansa

Kun ji cewa ana tsaka da wahalar tsadar rayuwa a Najeriya, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ba da shawara.

Akpabio ya ba yan kasar shawara wanda ya jawo ce-ce-ku-ce, yan Najeriya suka caccake shi da cewa yana musu isgilanci ne kan haka.

Hakan ya biyo bayan baram-barama da Akpabio ya yi a bidiyo da yake ba yan kasar shawara kada su yi wasa da duk inda suka abinci su ci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.