Bayan Rasa Rayuka a Jigawa, Barci Ya Dauke Direba, Wata Tankar Fetur ta Kama da Wuta

Bayan Rasa Rayuka a Jigawa, Barci Ya Dauke Direba, Wata Tankar Fetur ta Kama da Wuta

  • Jama'a na kukan iftila'in gobara da ya salwantar da rayuka sama da 100 a Jigawa, an karaa samun tankar fetur ta fadi a wata jiha
  • Lamarin ya afku da sanyin safiyar Laraba a lokacin da barci ya share matukin tankar mai har motar ta kwace daga hannunsa a Ogun
  • Hukumomi sun tabbatar da bayan kwacewar tankar ne sai ta kife, lamarin da ya jawo gagarumar gobara da ta haddasa dimbin asara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar OgunYayin da aka shiga jimamin rasa rayuka sama da 107 a Jigawa bayan fashewar tankar mai, wata tanka makare da fetur ta fadi a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Kwamitin Tinubu ya waiwayi masu kudi, ana shirin laftawa attajirai haraji

Da sanyin safiyar ranar Laraba ne tankar dauke da fetur ta fadi a yankin Ibafo a karamar hukumar Obafemi Owode a hanyar Legas zuwa Ibadan a Ogun.

Jihar Ogun
Tankar mai ta kama da wuta a Ogun Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Channels Television ta tattaro cewa bayan faduwar tankar, ta kama da wuta tare da lalata motoci da wasu ababen hawa masu tarin yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin faduwar tankar man fetur

Jaridar Punch ta wallafa cewa barci mai nauyi ya sace direban wata tanka makare da fetur lokacin da ya ke tsaka da tuki a jihar Ogun.

Lamarin ya jawo jirkicewar motar bayan ta kwacewa matukin, kuma kafin a ce kwabo sai ta fadi, ta na kamawa da wuta a bakin titi.

Jami’ai sun tabbatar da faduwar tankar fetur

Hukumar kare afkuwar hadurra ta jihar Ogun ta tabbatar da faduwar wata tanka dauke da man fetur, amma ta tabbatar cewa ba a samu asarar rayuka.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta karo kayan aiki domin ragargaje yan ta'adda a Arewa

Sai dai jami’in hulda da jama’a na hukumar, Babatunde Akinbiyi ya ce an yi asarar ababen hawa da lalata gine-gine, kuma tuni hukumar kashe gobara ta kai dauki.

Gobarar tankar fetur ta kashe mutum 107

A baya mun ruwaito cewa wata tankar fetur da ta fadi a jihar Jigawa ta jawo asarar rayukan bayanin Allah a lokacin da su ke tsaka da kwasar fetur da ya zube a kauyen Majiya.

Rahotanni sun tabbatar da zuwa yanzu an birne mutanen da su ka rigamu gidan gaskiya, yayin da sama da mutane 100 ke kwance a asibiti su na karbar magani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.