Ana Fama da Rayuwa, Gwamnatin Tinubu Na Neman Tatsar Kuɗi daga Ƴan Najeriya
- Nyesom Wike ya bukaci ƴan Najeriya su ba da haɗin kai wajen biyan haraji ga gwamnati domin a yi masu aiki
- Ministan ya ce masu surutun cewa gwamnati tumbin giwa ce don haka ba ta bukatar kuɗi ba su san abin da suke yi ba
- Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta fara shirin karɓar kashi 25% daga masu samun N100m zuwa sama a wata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce gwamnati a kowane mataki na bukatar tara kuɗin shiga domin yiwa talakawa aiki.
Nyesom Wike ya bayyana haka ne a wurin wani taro kan zuba hannun jari wanda wani kamfanin ya shirya a Abuja.
Gwamnatin Tinubu na bukatar tara kudi
Ministan harkokin Abuja ya ce tunanin da wasu ƴan Najeriya ke yi cewa gwamnati ba ta bukatar kuɗi ba gaskiya ba ne, kamar yadda Channels ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya kuma gargaɗi masu zuba hannun jari a Najeriya da cewa gwamnati ba za ta ci gaba da ba su biliyoyin Naira da filaye ba matuƙar ba za a samu riba ba.
Ministan Abuja ya gargaɗi masu zuba jari
"Wannan ya sa a yanzu gwamnati ta yi hankali, yanzu sai mun zauna mun duba idan muka saka kuɗinmu da filaye me zamu samu? Ba za mu ci gaba da saka dukiya ba tare da samun ko kwabo ba."
"Mutane suna yawan cewa gwamnati ba ta bukatar kuɗi, wa ya gaya maku haka? Idan gwamnati ba ta bukatar kudi to da me za a yi maku aiki?
"Shiyasa muka ce ku biya haraji, yana da matuƙar amfani. Bayan haka za mu ci gaba da karfafa wa masu zuba jari guiwa ta yadda za su samu riba ita ma gwamnati ta amfana."
- Nyesom Wike.
Kalaman Wike na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ke shirin sanya harajin kashi 25% ga attajiran da ke samun Naira miliyan 100 zuwa sama a Najeriya, in ji Leadership.
Dalilin Tinubu na ɗaukar tsauraran matakai
A wani rahoton kuma Gwamnatin Tarayya ta fadi dalilin da ya sa matakan da ake dauka a bangaren tattalin arziki suka kasance masu tsauri.
Shugaba Bola Tinubu ya ce babu yadda aka iya dole sai an ɗauki matakan ne domin tsamo kasar daga halin da take ciki
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng