Majalisa Ta yi Barazana ga Tinubu Yana Kasar Waje, Ta Bukaci Kasafin Kudi da Gaggawa

Majalisa Ta yi Barazana ga Tinubu Yana Kasar Waje, Ta Bukaci Kasafin Kudi da Gaggawa

  • An ruwaito cewa majalisar wakilai ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kasafin kudin shekarar 2025 mai kamawa
  • Majalisar ta bukaci Bola Tinubu ya gabatar mata da kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba domin ta samu damar yin bahasi a kansa
  • A yanzu haka dai shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutun mako biyu ƙasar Birtaniya, daga can kuma ya wuce kasar Faransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta ba shugaban kasa Bola Tinubu umarnin gaggawa kan kasafin kudi.

Majalisar ta bukaci Bola Tinubu ya gabatar mata da kasafin kudin shekara mai kamawa domin domin kaucewa jinkiri.

Kara karanta wannan

Daidaiton jinsi: Tinubu ya bayyana babban kudurin gwamnatinsa kan matan Najeriya

Tinubu
Majalisa ta bukaci Tinubu ya gaggauta gabatar da kasafin kudin 2025. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito majalisar na kokawa kan cewa fadar shugaban kasa ta yi jinkirin gabatar da kasafin kudin a bara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta ba Tinubu umarnin gaggawa

Majalisar wakilai ta yi kira na musamman ga Bola Tinubu kan gaggauta gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.

Yan majalisar wakilai sun ce sun yi kiran gaggawar ne saboda kaucewa jinkirin gabatar da kasafin kudin.

Wani dan majalisa, Cement Jumbo ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar kafin a tabbatar da shi.

Majalisa ta yi barazana ga Tinubu

Yayin da yake goyon bayan kudirin, Hon. Solomon Bob ya ce majalisar za ta iya kin amincewa da kasafin kudin idan Bola Tinubu ya yi jinkirin gabatar da shi.

A karkashin haka majalisar ta yi umarnin tabbatar da komai ya kammala cikin mako biyu domin kaucewa jinkiri.

Kara karanta wannan

An fadawa Tinubu ministan da zai kora yayin da 'yan Najeriya ke kwana a duhu

Amfanin gabatar da kasafin kudi da wuri

Majalisar wakilai ta ce gabatar da kasafin kudi a kan lokaci zai taimaka mata wajen nazari da yin cikakken bincike kan abin da ya ƙunsa.

Yan majalisa sun koka kan cewa ko a 2024 an makara wajen gabatar da kasafin kudin wanda ya kawo matsala a garesu.

Tinubu zai tura kudi ta asusun banki

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya na shirin fara raba kudi ga talakawan Najeriya domin rage radadin rayuwa.

Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana shirin Bola Tinubu na rabawa talakawa miliyan 20 tallafin kudi ta asusun banki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng