"Ban Samun Komai": Ministar Tinubu Ta Bayyana Kalubalen da Take Fuskanta

"Ban Samun Komai": Ministar Tinubu Ta Bayyana Kalubalen da Take Fuskanta

  • Mai girma Ministar mata ta Najeriya, Uju Kennedy-Ohanenye ta fito ta yi ƙorafi kan rashin samun kuɗi a ma'aikatarta
  • Ministar ta ce ba a ba ma'aikatar harkokin mata isassun kuɗi sannan wasu ayyyuka da take gudanarwa, da kanta ta ke yi
  • Uju Kennedy-Ohanenye ta yi waɗannan kalaman ne a wajen wani taron tara kuɗi domin shirin 'a bunƙasa ta' da aka ɓullo da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministar harkokin mata ta Najeriya, Uju Kennedy-Ohanenye, ta koka kan rashin samun kuɗi a ma'aikatarta.

Uju Kennedy-Ohanenye ta bayyana cewa babu wasu kuɗi da ke zuwa ma’aikatarta, kuma da kanta take ɗaukar nauyin wasu ayyukan.

Ministar mata ta koka kan rashin kudi
Uju Kennedy ta koka kan rashin kudi a ma'aikatar mata Hoto: @BarrUjuKennedy
Asali: Twitter

Ministar ta bayyana haka ne a yayin taron neman tara kuɗi domin shirin 'A bunƙasa ta' da aka gudanar a cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bindige 'yan bindigan da suka je karbar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi zaman ne ɗakin taro na Banquet dake fadar shugaban ƙasa a yammacin ranar Talata.

Minista ta yi ƙorafin kan rashin kuɗi

Da take magana da manema labarai, ministar ta ce an tara kuɗin ne domin al’amuran matan Najeriya maimakon ma’aikatar mata.

"Na samu kuɗi yau. Saboda mutane ƴan gulma masu son shiga abin da ba ruwansu a ciki, ina so na bayyana sarai cewa ba wai na tara wannan kuɗin ba ne domin ma’aikatar mata ba."
"Na tara wannan kuɗin ne domin harkokin matan Najeriya. Saboda abin da Shugaba Bola Tinubu ya ce a bar mata su sarara, za su sarara."
"Babu kuɗin da suke zuwa mani daga ma’aikatar domin na yi aiki. Duk abin da kuke gani, ina amfani da kuɗina ne domin gudanarwa."

- Uju Kennedy-Ohanenye

Ministar mata ta yiwa ƴan Najeriya albishir

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta gano babban kuskuren da 'yan Najeriya ke yi, ta yi gargadi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministar harkokin mata ta ba yan Najeriya hakuri tare da musu albishir da cewa wahala na dab da karewa.

Uju Kennedy Ohanenye ta ce Bola Tinubu na gyara kurakuren da aka yi a gwamnatocin baya ne kuma nan gaba kadan za a ga sauyi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng