Gwamna Ya Kirkiro Doka, Zai Karɓe Wani Kaso daga Kuɗin Kananan Hukumomi Duk Wata

Gwamna Ya Kirkiro Doka, Zai Karɓe Wani Kaso daga Kuɗin Kananan Hukumomi Duk Wata

  • Gwamnan Anambra ya kafa dokar rage wani kaso daga cikin kuɗin da gwamnatin tarayya za ta rika turawa kananan hukumomin jihar
  • Farfesa Charles Soludo ya ce yana ganin akwai matsala idan aka ba kananan hukumomi cikakken ikon cin gashin kansu
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun ƙoli ta yi hukuncin turawa kowace ƙaramar hukuma kudinta kai tsaye daga asusun tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya ce ba wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Soludo ya bayyana haka ne a ranar Talata a gidan gwamnati da ke Awka, bayan ya sanya hannu a kan kudirin dokar kananan hukumomin jihar Anambra.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisar PDP sun rasa kujerunsu, an ba INEC damar shirya sabon zaɓe

Gwamna Soludo.
Gwamna Soludo ya kafa dokar da za a rika rage kason kuɗin kananan hukumomi duk wata Hoto: Charles Soludo
Asali: Facebook

Gwamnan ya wallafa rubutaccen jawabin da ya yi bayan sa hannu a dokar a shafinsa na Facebook ranar Talata da yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Charles Soludo ya sa hannu kan dokar bayan majalisar dokokin jihar ta amince da ita duk da sukar da kudirin ya sha daga wasu ƴan majalisa.

Abin da dokar kananan hukumomin ta ƙunsa

Dokar dai ta tilastawa kowace ƙaramar hukuma a Anambra tura wani kaso na kuɗin da gwamnatin tarayya ta turo mata zuwa wani asusun haɗaka.

Gwamnatin jihar karkashin Soludo ce kaɗai ke ɗa ikon sarrafa wannan asusu na haɗaka da za a riƙa ajiye wani kaso daga kudin ƙananan hukumomi

Da yake jawabi bayan rattaɓa hannu kan dokar, Gwamna Soludo ya ce duk da kotun koli ta ba ƙananan hukumomi ƴanci da kyakkyawar niyya amma hakan zai kawo hatsaniya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya fadi lokacin gudanar da zaben ciyamomi

Gwamna Soludo ya hango matsala a kananan hukumomi

Soludo ya ce:

"Ba su cikakken ikon cin gashin kai na nufin kowace ƙaramar hukuma za ta yi nata tsarin, ta ɗauki malamai ta biya su albashi da sauran makamantansu.
"Hakan zai kawo cikas a abubuwa da dama a matakin ƙananan hukumomi kamar ɓangaren ilimin firamare da kananan asibitoci (PHC_."

Gwamna Soludo ya ƙara da cewa ya bullo da wannan dokar ne domin sa ido da kuma hana ciyamomi yin sama da faɗi da kuɗin talakawansu.

Gwamna zai fara biyan N70,000 a Anambra

A wani rahoton kuma Gwamna Soludo ya sanar da cewa zai fara biyan ma'aikatan jiharsa ta Anambra sabon albashin N70,0000 a watan Oktoba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da dukkanin shugabannin makarantun firamare da sakandare na jihar a Awka

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262