Ana ‘Lallaɓan’ Tinubu Ya Saki Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda, Bayanai Sun Fito

Ana ‘Lallaɓan’ Tinubu Ya Saki Ƙasurgumin Ɗan Ta’adda, Bayanai Sun Fito

  • An yi wani taro domin farfaɗo da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya a jihar Enugu a ranar Litinin da ta wuce
  • Jami'ar tarayya ta Nsukka da cibiyar samar da zaman lafiya ta USIP na cikin waɗanda aka yi hadaka da su wajen shirya taron
  • Yayin taron, an ba gwamnatin tarayya shawarar yadda za a samar da zaman lafiya a yankin na Kudu maso Gabashin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Ƙungiyar zaman lafiya ta SVCRG ta shirya taron zaman lafiya a jihar Enugu da ke kudancin Najeriya.

Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a samu hadin kai tsakanin al'umma da jami'an tsaro a Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

An fadawa Tinubu ministan da zai kora yayin da 'yan Najeriya ke kwana a duhu

Nnamdi Kanu
An bukaci a saki Nnamdi Kanu. Hoto: Radio Biafara
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa kungiyoyi sun bukaci gwamnatin tarayya ta canza salon samar da zaman lafiya a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bukaci gwamnatin Tinubu ta canza salon yaki

Kungiyoyin fararen hula sun bukaci gwamnatin tarayya ta canza salon yaki da yan ta'addan yankin Kudu maso Gabas.

Sun bukaci gwamnati ta daina amfani da karfin soja dari bisa dari wajen dakile masu tayar da kayar baya a yankin.

Ana so Tinubu ya saki Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar SVCRG, Farfesa Freedom Onuoha ya bukaci gwamnatin tarayya ta saki ƙasurgumin dan ta'adda, Nnamdi Kanu.

Farfesa Freedom Onuoha ya ce sun yi bincike sun gano cewa rike Nnamdi Kanu na cikin abubuwan da suke kara tayar da fitina ya yankin.

An ba gwamnoni shawara kan tsaro

Shugaban kungiyar USIP, Farfesa Chris Kwaja ya ce akwai bukatar sauya salon yaki da ta'addanci a yankin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

T-Pain da sauran sunaye 4 da aka lakawa Tinubu da dalilan alakanta shi da su

Saboda haka ya bukaci gwamnonin yankin da su hada kai wajen daukar matakin siyasa maimakon karfin bindiga kan magance rikicin yankin.

Birtaniya ta yi magana kan raba Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Birtaniya ta yi magana kan yunkurin dan a ware, Sunday Igboho na ware kasar Yarabawa daga Najeriya.

Birtaniya ta yi magana ne kan wata wasika da shugaban yan a waren ya rubuta mata domin neman goyon bayan ficewar Yarabawa daga Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng