"Zaman Lafiya": Ana Tsaka da Rikicin NNPP, Gwamma Abba Ya Taɓo Fulani a Kano

"Zaman Lafiya": Ana Tsaka da Rikicin NNPP, Gwamma Abba Ya Taɓo Fulani a Kano

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga Fulani su zauna lafiya da kowa a Kano musamman abokan zamansu Hausawa
  • Abba ta bakin kwamishinan ayyuka na musamman, Usman Aliyu, ya buƙaci Fulani, Hausawa da sauran ƙabilu su rungumi zaman lafiya
  • Haka kuma shugaban jami'ar tarayya ta Kashere, Farfesa Umar Pate ya ce bai dace a jingina kalubalen tsaron kasar nan ga ƙabila ɗaya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci Fulani su zauna lafiya da sauran abokan zamansu a faɗin jihar Kano.

Abba Kabir ya faɗi haka ne a wurin taron bikin Pulako na ƙasa wanda ƙungiyar raya al'adun Fulani ta Fulbe reshen Kano ta shirya ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 4 da ake zargi da rushe kadarori a jihohinsu kan bambancin siyasa

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan Kano ya roki Fulani su zauna lafiya da kowa a jihar Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce gwamnan wanda kwamishinan ayyuka na musamman, Usman Aliyu ya wakilta, ya ce zaman lafiya shi ne abu na farko da ya kamata Fulani su ba fifiko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya roki Hausawa, Fulani su zauna lafiya

Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ta ɗauki al'adun Fulani da muhimmanci kuma suna taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya kuma yi nuni da muhimmancin alaƙa da zumunci tsakanin Fulani da Hausawa, inda ya roƙi su zauna lafiya da kuma mutunta juna.

"An san Fulani da ƙaunar zaman lafiya, don haka ya zama tilas mu guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya a cikin al'ummarmu. 
"Ku zo mu haɗa hannu da sauran ƙabilu domin gina gobe mai kyau ga jiharmu da ma ƙasa baki ɗaya," in ji gwamnan.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Gwamna Abba ya juyawa Kwankwaso baya kan mutum 2 a Kano

'Ba Fulani kaɗai ne matsalar Najeriya ba'

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban jami'ar tarayya ɗa ke Kashere a jihar Gombe, Farfesa Umar Pate ya ce bai kamata a ɗora laifin kalubalen tsaro kan ƙabila ɗaya ba.

Ya yi kira da a hada kai tare da tabbatar da adalci a tsakanin ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Farfesa Umar ya kuma yi nuni da irin arzikin da Fulanin ke da shi wanda ya kunshi shanu, ya jaddada bukatar samar da filayen kiwo don tallafa wa rayuwarsu.

Rikicin NNPP: Gwamna Abba ya tafi Abuja

A wani rahoton kuma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shilla zuwa birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2024.

Abba Kabir Yusuf ya fice daga jihar ne yayin da ake ci gaba da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262