Farashin fetur: NNPCL Ya Musanta Cimma Yarjejeniya da IPMAN, Ya Bayyana Yadda Abin Yake

Farashin fetur: NNPCL Ya Musanta Cimma Yarjejeniya da IPMAN, Ya Bayyana Yadda Abin Yake

  • Kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya yi magana kan batun cimma yarjejeniya da ƴan kasuwa kan farashin fetur
  • Babban daraktan yaɗa labarai na NNPCL ya ce babu wata yarjejeniya da suka cimmawa tsakaninsu da ƙungiyar IPMAN
  • Olufemi Soneye ya ce a yanzu kasuwa ce take ƙayyaɗe farashin da za a siyar da man fetur ba wai kamfanin NNPCL ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya musanta iƙirarin cimma yarjejeniyar farashin mai da kungiyar dillalan mai ta Najeriya (IPMAN).

Tun da farko, shugaban ƙungiyar IPMAN, Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa kamfanin na NNPCL ya amince da rage farashin litar man fetur daga N958 zuwa N955.

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Ministan Tinubu ya fadi dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka daina korafi

NNPCL ya musanta cimma yarjejeniya da IPMAN
NNPCL ya musanta cimma yarjejeniya da IPMAN kan farashin fetur Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Sai dai, babban daraktan yaɗa labarai na kamfanin na NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana cewa ko kaɗan babu irin wannan yarjejeniyar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPCL ya musanta yarjejeniya da IPMAN

Soneye ya bayyana cewa, a ƙarƙashin tsarin da ake a halin yanzu, yanayin kasuwa ne ke yanke farashin mai, ba wai ta hanyar yarjejeniya tsakanin NNPCL da ƴan kasuwa ba.

"Babu yarjejeniyar farashi tsakanin IPMAN, NNPCL, ko wani ɗan kasuwa. Yanayin kasuwa ne yanke farashin a ƙarƙashin tsarin da ake kai a halin yanzu."

- Olufemi Soneye

NNPCL: Abin da ya faru da yan kasuwa

Ya kuma ƙara da cewa kamfanin na NNPCL ya bayar da rangwamen N3 ne kawai sau ɗaya ga ƴan kasuwan da suka ajiye kuɗaɗensu a NNPCL domin saukaka jigilar man da kuma hana ƙarancinsa.

Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne kawai na wucin gadi domin kamfanin NNPCL yanzu ba shi ba ne yake ƙayyade farashin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Rabuwar PDP: Gwamnan Bauchi ya bayyana makomar rikicin da ya addabi jam'iyya

Shugaban NNPCL ya faɗi ribar fasa ƙwaurin mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ce masu fasa ƙwaurin fetur sun yi amfani da tallafin da gwamnati ta riƙa biya wajen samu riba.

Mele Kyari ya bayyana cewa sakamakon biyan tallafin, masu fasa ƙwaurin na samun ribar kusan N17m kan kowace babbar mota da aka kai zuwa ƙasashe makwabta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng