Rikicin Jam'iyya: An Bayyana Lokacin da Damagum Zai Sauka daga Shugaban PDP

Rikicin Jam'iyya: An Bayyana Lokacin da Damagum Zai Sauka daga Shugaban PDP

  • Gwamnonin PDP sun dauki manyan matakai yayin da rikicin jam'iyyar ya kara ƙamari wanda ya kai ga an samu rabuwar kawuna
  • An rahoto cewa gwamnonin sun amince Umar Damagum ya ci gaba da zama matsayin shugaba zuwa ranar 24 ga Oktobar 2024
  • An ce a ranar ne ake sa ran PDP za ta gudanar da taron kwamitin zartarwa inda za a zabi sabon shugaba daga Arewa ta tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam'iyyar PDP ta sake daukar zafi a wannan makon yayin da jiga-jiganta ke ci gaba da rigima kan shugabanci da kuma nuna karfin iko.

A ranar Talata ne aka rahoto cewa an ba shugaban PDP na kasa, Umar Damagum damar sauka daga kujerarsa a mako mai zuwa.

Kara karanta wannan

Rabuwar PDP: Gwamnan Bauchi ya bayyana makomar rikicin da ya addabi jam'iyya

Gwamnonin PDP sun ba Damagum 'yar karamar dama kafin saukarsa daga shugaban jam'iyya
Ana sa ran mako mai zuwa Damagum zai sauka daga shugaban jam'iyyar PDP. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa gwamnonin jam’iyyar sun cimma matsayar sauke Damagum daga kujerarsa ne a a jiya a Akure, babban birnin jihar Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP sun bayyana fargabarsu

Majiyoyin da ke da cikakken bayanin taron da kuma wani taron tattaunawa da aka gudanar a ranar Litinin ta intanet sun ce gwamnonin sun dauki maganar da gaske.

Majiyoyin sun bayyana cewa gwamnonin sun yi kaca-kaca da tsagin kwamitin gudanarwar PDP na kasa (NWC) tare da yanke shawarar hada kai domin magance rikicin jam’iyyar.

A yayin taron na ranar Litinin, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda rikicin ya jawo rabuwar kawuna a kwamitin NWC.

Adeleke ya bayyana fargabar cewa rikicin na iya kawo cikas ga yunkurinsa na neman tazarce a 2026, kasancewar shi ne na farko a cikin gwamnonin da za su sake yin takara.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun raba gardama, sun sanar da sahihin shugaban jam'iyya na ƙasa

Gwamnoni sun yanke makomar Damagum a PDP

Gabanin kaddamar da yakin neman zaben gwamnan PDP na jihar Ondo, gwamnonin sun amince Damagum ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa 24 ga Oktoba.

An tattaro cewa Damagum da Ambasada Taofeek Arapaja, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa (shiyyar Kudu) sun halarci taron na jiya Talata.

Gwamnonin sun amince cewa yayin da Damagum ke ci gaba da zama shugaban riko na ‘yan kwanaki masu zuwa, za a yi amfani da taron kwamitin zartarwa na kasa wajen fito da shugaba daga Arewa ta tsakiya.

Bugu da kari, taron ya ba da shawarar umartar 'yan jam'iyyar da su janye duk wasu kararrakin da ke gaban kotu da suka shafi rikicin shugabancin PDP na kasa.

An dakatar da Damagum, Anyanwu a PDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa wani tsagin kwamitin gudanarwar PDP ya dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Umar Damagum da kuma sakataren kasa, Samuel Anyanwu.

Kara karanta wannan

An gano gwamnonin PDP da ke son tsige Damagum, an gaza cimma matsaya

A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaran PDP, Debo Ologunagba ya fitar, tsagin ya ce ya dakatar da Damagum da Anyanwu saboda kin biyayya ga dokokin jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.