Tsohon Sanata Ya Caccaki Bankin Duniya, Ya Fadi Illar Amfani da Manufofin Tinubu
- Tsohon Sanata, Shehu Sani ya bayyana takaicin shawarar da Bankin Duniya ya bayar kan farfado da tattalin arzikin kasa
- Mataimakin shugaban bankin ne ya nemi kasar nan ta cigaba da amfani da manufofin Bola Ahmed Tinubu na shekaru 10-15
- Sanata Shehu Sani ya gano illar da ke tattare da shawarar, inda ya ce kafin lokacin, yan kasar nan sun kusa gama mutuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana rashin gamsuwa da shawarar da Bankin Duniya ya ba kasar nan kan bunkasar tattalin arziki.
Mataimakin shugaban bankin, Mista Indermit Gill ne ya ce kasar nan na bukatar cigaba da amfani da manufofi irin na shugaba Bola Tinubu na tsawon shekaru 15.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa da alama Bankin Duniya na son yan Najeriya su cigaba da azabtuwa har na tsawon shekarun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bankin Duniya ba shi da amfani:" Tsohon Sanata
Tsohon Sanata, Shehu Sani ya bayyana rashin amfanin Bankin Duniya wajen cicciba kasashe masu tasowa daga talauci zuwa samun yalwa.
Sanata Shehu Sani wanda ya yi mamakin shawarar da bankin ya ba gwamnatin Najeriya, ya nemi sanin kasashe nawa bankin ya ceto daga talauci.
Sanata Shehu Sani ya caccaki manufofin Tinubu
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ba lallai a samu yan Najeriya da yawa ba idan har sai an kai shekaru 15 kafin manufofinsa su ceto kasar nan.
" Ban san mutane nawa ne za su rage ba a lokacin domin sharbar romon Bankin Duniya ke albishir a kai," cewar Sanata Shehu Sani.
Bankin Duniya ya yi na'am da manufofin Tinubu
A baya mun wallafa cewa Bankin Duniya ya bayyana goyon baya ga manufofin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke bijirowa da su wajen magance wahalhalun da kasar nan ke ciki.
Mataimakin shugaban bankin, Mista Indermit Gill ne ya bayyana goyon bayansa, ya ce kamata ya yi a cigaba da manufofin gwamnatin tarayya na tsawon shekaru 10 zuwa 15.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng