"A Dage da Addu'a": Malami Ya Hango Wata Jiha da Za Ta Fuskanci Girgizar Kasa

"A Dage da Addu'a": Malami Ya Hango Wata Jiha da Za Ta Fuskanci Girgizar Kasa

  • Fitaccen malamin nan, Primate Elijah Ayodele, ya ce nan ba da dadewa ba 'yan Legas za su fuskanci karamr girgizar kasa
  • A wani sabon faifan bidiyo da Legit Hausa ta gani, malamin ya roki al’ummar Legas da su dage da addu’a a kan girgizar kasar
  • A makonnin da suka gabata ne aka samu rahoton afkuwar karamar girgizar kasa a sassan Abuja na tsawon kwanaki biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas – Shugaban cocin Inri Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya ce mutanen Legas na iya fuskantar karamar girgizar kasa nan ba dadewa ba.

Primate Ayodele ya roki mazauna Legas da su dage da yin addu'a kan wannan musiba da ke shirin afkuwa.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da wani gini mai hawa 2 ya rufta, bidiyo ya bayyana

Malamin addini ya yi magana kan yiwuwar samun girgizar kasa a jihar Legas
Primate Ayodele ya ce nan ba da jimawa ba za a iya samun girgizar kasa a Legas - Hoto: @primate_ayodele
Asali: Facebook

'A dage da addu'a' - Malamin coci

A cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, 15 ga Oktoba, malamin ya ce bai san taka-mai-mai ranar da abin zai faru ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Primate Elijah Ayodele:

“A jihar Legas, mu dage da addu’a kan girgizar kasa da ke shirin afkuwa. Yana da muhimmaci sosai. Ba ni da masaniya game da rana da lokacin da abin zai afku."

Girgizar kasa a Najeriya

An fara samun rahoton afkuwar girgizar kasa a Najeriya a 1933. An kuma bayar da rahoton faruwar hakan a 1939, 1964, 1984, 1990, 1994, 1997, 2000 da 2006, inji rahoton IAEA.

An rahoto cewa Najeriya na samun karancin girgizar kasa saboda tana a wani bigire a nahiyar Afrika da ke takaita ayyukan da ke jawo girgizar kasar.

Kara karanta wannan

Ana kokarin shawo kan tsadar fetur, farashin gas din girki ya lula sama

Babban birnin Najeriya, Abuja na fuskantar karamar girgizar kasa a kai a kai.

Hakazalika, mazauna wani gari a jihar Oyo, Saki, sun taba shaida karamar girgizar kasa kamar yadda aka rahoto.

An samu afkuwar girgizar kasa a Abuja

Tun da fari, mun ruwaito cewa mazauna unguwar Mpape a karamar hukumar Bwari a Abuja sun shiga firgici sakamakon karamar girgizar kasa da ta afku na kwanaki biyar a jere.

Wani mazaunin unguwar, Obinna Ngozi ya ce gine-gine na girgiza a duk lokacin da kasar ta motsa, lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.