Jagororin APC Sun Ba 'Yan Najeriya Shawara kan Gwamnatin Tinubu

Jagororin APC Sun Ba 'Yan Najeriya Shawara kan Gwamnatin Tinubu

  • Wasu jagororin jam'iyyar APC a jihar Legas sun ba ƴan Najeriya shawara kan gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Jiga-jigan na APC sun bayyana cewa raɗaɗin da ake sha a ƙasar nan mai wucewa ne domin za a samu sauƙi a nan gaba
  • Sun yi nuni da cewa Shugaba Tinubu gyara yake yi a ƙasar nan domin gwamnatocin baya sun lalata ba su yi abin da ya dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Jagororin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Somolu da ke jihar Legas, sun bukaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jagororin na APC sun buƙaci ƴan Najeriya musamman matasa da ka da su yi watsi da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon mataimakin gwamna da wasu mutum 6

Jagororin APC sun ba 'yan Najeriya hakuri
Jagororin APC sun bukaci a kara hakuri da gwamnatin Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Jiga-jigan na APC sun bayyana hakan ne a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da manema labarai a Legas, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin APC sun ba ƴan Najeriya haƙuri

Ɗaya daga cikinsu, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Somolu, Mista Olorogun Bagostowe, ya ce ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu ba zai ɗore ba, rahoton PM News ya tabbatar.

Bagostowe, wanda ya kwatanta ƙalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta a yanzu da wuyar da mace mai ciki ke sha kafin haihuwar jaririnta, ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba ƴan Najeriya za su manta da raɗaɗin da suke ciki.

"Ya kamata jama’ar mu su kwantar da hankalinsu, domin an bar Najeriya ta lalace a tsawon shekara 60 da suka gabata."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Dan majalisa ya fadi abin da ya kamata a yi wa Tinubu

"Abin da ya kamata gwamnatocin baya su yi a shekara 60 da suka gabata, su ne abubuwan da Shugaba Bola Tinubu ke ƙoƙarin yi da manufofinsa."
"A yanzu manufofin za su iya zama masu tsauri, amma a ƙarshe za su amfani ƴan Najeriya."
"Ina so na gayawa mutanenmu, musamman matasa, su kwantar da hankalinsu. Al'amura za su daidaita."

- Olorogun Bagostowe

Tinubu ya magantu kan tallafin mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan tsare tsaren gwamnatinsa musamman cire tallafin man fetur.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce dukkan matsalolin da mutane suke gani sun addabi Najeriya, tabbas za a iya magance su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng