An Cafke Barayin Babur da Suka Sassara Dattijo Dan Shekaru 60 da Adda

An Cafke Barayin Babur da Suka Sassara Dattijo Dan Shekaru 60 da Adda

  • Rundunar yan sandan Najeriya a Ogun ta yi nasarar cafke wasu gungun mutane da ake zargi da satar babur a hannun wani dattijo
  • An ruwaito cewa barayin sun buya a jeji ne yayin da dattijon ya zo wucewa, sai suka fito suka tare shi suka fara harbinsa da bindiga
  • Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ta kama mutanen da ake zargin da makaman da suka yi amfani da su wajen kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Ogun sun samu nasarar cafke wasu da ake zargi da satar babur.

Rahotanni sun nuna cewa barayin sun tare wani dattijo ne a yankin Owodo Egba a kan hanyar Ajura zuwa Shiun.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ƙawanya a kauye cikin dare, sun kashe mutane

Jihar Ogun
An kama barayin babur a Ogun. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar the Guardian ta tabbatar da cewa a ranar Litinin yan sanda suka cafke mutanen da ake zargi da satar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama barayin babur a Ogun

Rundunar yan sanda a jihar Ogun ta cafke wasu mutane uku da ake zargi sun shahara da satar abin hawa wajen al'umma.

Ana zargin cewa mutane ukun sun tare wani dattijo dan shekaru 60 da masa ta'addanci yayin da yake wucewa a kan babur.

Barayi sun sassara dattijo mai shekaru 60

A yayin da dattijo mai suna Rotimi Bajela zai wuce a kan babur barayin suka fito a kan titi suka fara harbin shi da bindiga.

Bayan sun ga harbin bindigar bai kashe dattijon ba sai suka ciro adda suka fara sassara shi a kai da wuya.

A yayin da suka jikkata dattijon mai shekaru 60, barayin sun kwace masa babur, kudi da wayar hannu ƙirar Itel.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun farauto gawurtattun yan fashi da makami

Yan sanda sun kama barayin babur

Kakakin yan sandan jihar Ogun, Omolola Otudola ta tabbatar da cewa sun yi nasarar cafke barayin da ake zargi da satar.

Daily Post ta ce Omolola Otudola ta bayyana cewa an kama barayin ne bayan samun bayanan sirri da aka yi a kansu kuma yanzu haka ana bincikensu.

An kashe babban ɗan sanda a Delta

A wani rahoton, kun ji cewa wani babban dan sanda ya rasa ransa yayin da ya jagoranci runduna domin fada da yan bindiga a Delta.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa dan sandan ya rasa ransa yayin da suka yi artabu da yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng