Son zuciya bacin zuciya: Yansanda sun yi caraf da barayin babur 2, daya ya mutu a gudun tsira

Son zuciya bacin zuciya: Yansanda sun yi caraf da barayin babur 2, daya ya mutu a gudun tsira

Dubun wasu barayin babur da suka shahara wajen satar baburan jama’a suna tsallakawa dasu kasar Nijar da nufin siyar ta cika, inda wasu guda biyu suka fada komar jami’a Yansandan Najeriya, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen barayin kamar haka: Evans Ajao da Isaiah Aigba. Haka zalika rundunar Yansandan jihat ta bayyana cewa wani barawon babur ya gamu da ajalinsa a yayin gudun tsira a garin Abekuta, a ranar Asabar 28 ga watan Afrilu, bayan ya bindige mai babur din, shi kua yayi hatsari ya mutu.

KU KARANTA: Yadda wata Budurwa ta yanke mazakutan Saurayinta da almakashi bayan ya fitar da bidiyon kwanciyarsu

Kaakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da haka, inda yace Ajao da Aigba sun shiga hannu ne a ranar Larabar data gabata, a kauyen Baagbon dake cikin karamar hukumar Odede na jihar Ogun, inda suka kama su dauke da babur, kirar Bajaj.

Son zuciya bacin zuciya: Yansanda sun yi caraf da barayin babur 2, daya ya mutu a gudun tsira
Barayin

“Bincike da muka gudanar dakan barayin sun bayyana mana cewar suna da masu siya a kasar Kwatano, kuma sun dade sun satar babura, kwamishinan Yansandan jihar Ahmed Iliyasu ya umarci a mika barayin zuwa hannun Yansandan SARS don gudanar da bincike.”

Kaakaki Oyeyemi ya cigaba da cewa: “Barawon ya yi badda kama be kamar wani Fasinja, amma a yayin da suka fara tafiya sai ya ciro bindiga ya umarci dan achabar mai suna Toyin Ayade ya sauka, anan suka fara darga, inda dan fashin ya bingide shi a hannu, ya kuma dauke babur, daga nan jama’a suka bi shi, inda ya fada cikin rami, ya buge kansa da kankare, nan take ya garzaya barzahu."

Daga karshe Kaakakin yace sun gano bindiga guda daya, alburusai da dama, sai kuma babur din da ya sata, sa’annan wanda aka yi ma fashin na samun kulawa a Asibiti, kuma yana farfadowa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel