Gwamnatin Tarayya Ta Gano Wani Babban Kuskure da 'Yan Najeriya ke Yi, Ta Yi Gargadi

Gwamnatin Tarayya Ta Gano Wani Babban Kuskure da 'Yan Najeriya ke Yi, Ta Yi Gargadi

  • Gwamnatin tarayya ta nuna takacinta kan yadda wasu ƴan Najeriya ke faɗar abubuwa marasa kyau game da ƙasar nan
  • Mahukunta sun yi gargaɗi kan yin hakan inda aka nuna cewa hakan yana taɓa ƙima da martabar ƙasar nan a idon duniya
  • Ministan yaɗa labarai wanda ya bayyana hakan ya ce ɓata sunan ƙasar nan na sanyawa masu zuba hannun jari su ƙi shigowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta gargaɗi ƴan Najeriya kan ɓata sunan ƙasar nan.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yin hakan yana hana masu zuba hannun jari da masu zuwa yawon buɗe ido shigowa ƙasar nan.

Gwamnati ta yi gargadi kan bata sunan Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bukaci a daina bata sunan kasar nan Hoto: @FMINONigeria
Asali: Twitter

Gwamnati ta koka kan ɓata sunan Najeriya

Kara karanta wannan

Sanata ya fallasa rawar da 'yan siyasa ke takawa kan shan miyagun kwayoyi

Jaridar The Punch ta ce ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro a birnin tarayya Abuja, a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed Idris ya bayyana cewa idan ƴan Najeriya suka ci gaba da faɗar munanan kalamai a kan ƙasar nan, hakan zai sanya masu zuba hannun jari ƴan ƙasashen waje su ƙi zuwa Najeriya.

Ministan ya ce ɓata sunan ƙasar nan ba abu ba ne wanda ya kamata a ce ƴan Najeriya na yi, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

Gwamnatin tarayya ta ja kunnen ƴan Najeriya

"Hakan ya sa na yi nazari kan yadda ƴan Najeriya ke magana a kan ƙasarsu. Mu ne muke fafutukar ganin masu zuba hannun jari sun shigo ƙasar nan."
"A ɗaya ɓangaren kuma, muna saurin faɗin abubuwan da za su kori masu zuba hannun jari da waɗanda ke son yin hulɗa da mu."

Kara karanta wannan

Mohammed Yayari: Dalilin naɗa sabon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa ya bayyana

"Dole ne mu samo hanyar da za mu samu daidaito, musamman kafafen yaɗa labarai su riƙa ba da rahotanni na gaskiya tare da nuna ƙishi ga ƙasarsu."
"Na sha faɗin cewa babu yadda za a yi ka tallata ƙasar ka yayin da kake faɗin abubuwa marasa kyau a kanta. Saboda haka akwai buƙatar mu riƙa tallata ƙasar nan ta hanyar da ta dace."

- Mohammed Idris

NNPP ta ba gwamnatin Tinubu shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta yi kira ga Bola Tinubu da ya nemi taimakon tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Sakataren jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dipo Olaoyoku, ya bayyana cewa a fili yake gwamnati mai ci ba ta da isassun dabarun yadda za a fitar da Najeriya daga cikin ƙunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng