Ana Batun Warware Rikicin PDP, 'Yan Daba Sun Farmaki Sakatariyar Jam'iyyar

Ana Batun Warware Rikicin PDP, 'Yan Daba Sun Farmaki Sakatariyar Jam'iyyar

  • Ƴan daba sun kai farmaki a ɗaya daga cikin sakatariyoyin jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Benue a yankin Arewa ta Tsakiya
  • Ƴan daban sun kutsa cikin sakatariyar da ƙarfin tsiya inda suka kwashe kayayyki da wasu takardu a ofisoshin da ke cikinta
  • Sakatariyar dai ta ɗaya daga cikin ɓangaori biyu na jam'iyyar ne bayan rikicin cikin gida ya sanya ta dare zuwa gida biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu ƴan daba sun kai hari a sakatariyar jam’iyyar PDP a jihar Benue da ke lamba 1 a titin Ochagwu Lawani Street, New GRA, a Makurdi.

Sakatariyar dai ta wani tsagin jam'iyyar PDP ne wacce ke adawa a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Kara karanta wannan

Rabuwar PDP: Gwamnan Bauchi ya bayyana makomar rikicin da ya addabi jam'iyya

'Yan daba sun farmaki sakatariyar PDP a Benue
'Yan daba sun farmaki sakataroyar jam'iyyar PDP a Benue Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan daba sun farmaki sakatariyar PDP

Jaridar The Nation ta ce mai taimakawa Sanata Gabriel Suswam kan harkokin yaɗa labarai, Bede Bartholomew ya ce maharan sun zo ne a cikin motoci uku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa sun farfasa ƙofar shiga sakatariyar sannan suka shiga ofisoshin da ke ciki da ƙarfin tsiya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Sun yi sata a ofisoshin tare da kwashe wasu takardu zuwa cikin motocinsu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe."
"Maharan sun kwashe kayayyaki tare da takardu a sakatariyar, inda suka loda su a manyan motoci."
"Hotunan CCTV sun nuna fuskokin maharan, inda aka gano wasu mutane uku tare da cafke wasu daga cikinsu."

- Bede Bartholomew

Jam’iyyar PDP a jihar Benue dai ta rabu gida biyu, kowane ɓangare yake da sakatariyarsa a birnin Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya yabi ministan Tinubu, ya fadi nasarorin da ya samu

Karanta wasu labaran kan jam'iyyar PDP

Jam'iyyar PDP ta warware rikicinta

A wani labarin kuma, kun ji shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana kan rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar.

Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnonin PDP sun sasanta rikicin samun ɓangarori da ya shafi kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa (NWC).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng