Malaman Musulunci a Kano Sun Haɗa Kai, Sun Aika Saƙo ga Mutanen Jihar Borno

Malaman Musulunci a Kano Sun Haɗa Kai, Sun Aika Saƙo ga Mutanen Jihar Borno

  • Malaman addinin Musulunci a Kano sun ba mutanen da ambaliya ta shafa a Borno tallafin abinci da kayayyakin N140m
  • Tawagar wakilan malamai da kungiyoyin Musulunci sun kai ziyarar jaje ga Gwamna Babagana Zulum bisa ibtila'in da ya afku
  • Gwamna Zulum ya godewa malaman bisa wannan tallafi da kuma ware lokaci da suka kai ziyara domin jajantawa jihar Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Malamai da kungiyoyin addinin Musulunci a jihar Kano sun haɗa kayayyakin da suka kai N140m, sun aikawa mutanen da ambaliya ta shafa a Borno.

Malaman Musuluncin sun haɗa kayayyakin da suka kunshi abinci domin ragewa mutanen da mummunar ambaliya ta yi wa ɓarna a Maiduguri da kewaye.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun raba gardama, sun sanar da sahihin shugaban jam'iyya na ƙasa

Taswirar Kano.
Malaman Musulunci a Kano sun haɗa kayan N140m, sun ba mutanen da ambaliya ta shafa a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Malaman Kano sun tura tawaga zuwa Maiduguri

Daily Trust ta ce tawagar wakilan malaman Kano karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Babangida sun je yi wa gwamna Babagana Zulum jaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi yayin ziyarar da suka kai wa Gwamna Zulum a Maiduguri, Farfesa Muhammad ya ce mutanen Borno sun fuskanci jarabawa da dama.

Ya ce tallafin da malaman Kano da kungiyoyin Musulunci suka haɗa ba shi da yawa idan aka duba mummunar ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yiwa mutane.

Malaman musulunci sun yabawa Gwamna Zulum

Farfesa Muhammad Babangida ya ce:

"Abin da aka rasa ba zai misaltu ba, mutanen Borno kuna yawan shiga jarabawa tun daga matsalar Boko Haram, gobara a kasuwanni yanzu kuma ga ambaliya.
"Ba don Allah ya ba ku gwamna mutumin kirki ba da ba mu san irin halin da za a shiga a jihar nan ba, abin sai ya fi haka muni.

Kara karanta wannan

Mummunar ambaliyar ruwa ta jefa mutane miliyan 2 cikin babbar matsala a Arewa

"Ina rokon ka (Zulum) ka da ka bari sheɗan ya rinjaye ka, ka daina ayyukan alherin da kake yi."

Da yake nasa jawabin Gwamna Zulum ya gode musu bisa wannan gudummawar da kuma yadda suka ware lokaci suka kawo ziyar jihar Borno, rahoton Punch.

Cutar kwalara ta bulla a Borno

A wani labarin kuma gwamnatin Borno ta bayyana cewa an samu ɓullar kwalara a wasu ƙananan hukumomi sakamakon ambaliyar ruwa.

Kwamishinan lafiya, Farfesa Baba Gana ya ce gwamnati ta fara kokarin yaƙar cutar tun da wuri domin daƙile yaɗuwarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262