Yan Bindiga Sun yi Ƙawanya a Kauye cikin Dare, Sun Kashe Mutane

Yan Bindiga Sun yi Ƙawanya a Kauye cikin Dare, Sun Kashe Mutane

  • Yan bindiga sun kara kai mummunan hari wani ƙauye a jihar Filato inda suka kashe wasu mutane ciki har da wani dattijo
  • Rahotanni sun nuna cewa miyagu yan bindigar sun fitini mutanen kauyen Rafut da munanan hare hare cikin yan kwanakin nan
  • Mutanen ƙauyen Rafut sun ce ko a ranar 12 ga watan Oktoba sai da yan bindiga suka kai wani hari da ya jawo asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Rahotanni da suka fito daga jihar Filato na nuni da cewa yan bindiga sun kai hari wani ƙauye.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Rafut da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato da ke Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi artabu tsakanin bangarori 2 na yan bindiga da suka farmaki sakatariyar APC

Filato
Yan bindiga sun kai hari Filato. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kungiyar yankin, Farmasun Fuddang ne ya tabbatar mata da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kashe mutane 4

A ranar Litinin da dare wasu yan bindiga suka yi kwanton ɓauna a kan wasu matasa masu gadin gidajensu a kauyen Rafut.

Miyagu yan bindigar sun yi nasarar hallaka masu gadin su hadu nan take kafin su wuce wani gidan domin yin ta'addanci.

Yan bindiga sun kashe dattijo a kauye

Biyo bayan kashe masu gadin gidajen, an ruwaito cewa yan bindigar sun nufi wani gida da wani dattijo ke zaune.

Da isar yan bindigar wajen suka bude wuta ga dattijon kuma haka suka tafi ba tare da an kama ko daya daga cikinsu su ba.

Yadda yan bindiga suka matsawa kauye

Mutanen yankin Rafut sun ce a ranar 7 ga Oktoba an kashe musu mutane biyar, a ranar 10 ga Oktoba kuma an kashe musu mutane hudu.

Kara karanta wannan

An harbe shugaban yan sanda da wasu jami'ai yayin artabu da yan bindiga

Haka zalika sun bayyana cewa an kashe musu mutum daya a ranar 11 ga Oktoba haka zalika a ranar 12 ga Oktoba.

Mutanen yankin sun yi Allah wadai da hare haren da ake yawan kai musu da kuma kira ga hukumomi da su kai musu dauki.

Yan fashi sun kai hari Akwa Ibom

A wani rahoton, kun ji cewa yan fashi da makami sun mamaye wata unguwa a yankin jihar Akwa Ibom har suka yi sata sosai.

Rahotanni sun nuna cewa yan fashi da makamin sun harbi wata mata kuma sun yi wa mijinta barazanar kisa yayin harin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng