‘Fetur zai Sauka,’ IPMAN Ta yi Bayani bayan Cimma Matsayar Farashi da NNPCL

‘Fetur zai Sauka,’ IPMAN Ta yi Bayani bayan Cimma Matsayar Farashi da NNPCL

  • An samu daidaito kan farashin litar man fetur tsakanin kamfanin man Nigeria na NNPCL da kungiyar yan kasuwa ta IPMAN
  • Hakan ya biyo bayan saka baki da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi ne tsakanin kamfanin NNPCL da kungiyar IPMAN
  • Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, Hammed Fashola ya ce akwai yiwuwar samun sauƙin farashin litar man fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kamfanin NNPCL da kungiyar yan kasuwar man fetur sun cimma matsaya kan farashin litar mai.

Rahotanni sun nuna cewa an samu daidaiton ne bayan shiga tsakani da hukumar DSS ta yi kan lamarin.

Gidan mai
NNPCL da IPMAN sun cimma matsaya kan farashin man fetur. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa mataimakin shugaban kungiyar IPMAN, Hammed Fashola ya yi godiya ga hukumar DSS.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fetur: IPMAN da NNPCL sun cimma matsaya

Bayan samun daidaito tsakanin IPMAN da NNPCL, kamfanin NNPCL zai sayar da litar mai ga kungiyar IPMAN a kan N995.

Kungiyar IPMAN ta ce sun samu nasarar warware da yawa daga cikin matsalolin da suka samu da NNPCL kan man fetur.

Nawa sabon farashin mai zai kasance?

Biyo bayan sulhun, mataimakin shugaban IPMAN, Hammed Fashola ya ce za a samu saukin farashin litar man fetur ko da kadan ne.

Fashola ya ce duk da akwai matsalar nisa daga wasu jihohi hakan ba zai hana a samu sauƙin farashin litar man fetur ba.

Ya ce za su zauna a kungiyance domin duba yadda za su fitar da bayani a kan yadda farashin mai zai kasance a wajensu.

Kungiyar IPMAN ta yi godiya ga DSS

Kungiyar IPMAN ta mika godiya ga hukumar DSS kan yadda ta jajirce wajen sasanta tsakanita da kamfanin NNPCL.

Kara karanta wannan

DSS ta shiga tsakani kan rigimar kungiyar IPMAN da NNPCL, an samu matsaya

TVC ta ce Hammed Fashola ya ce duk inda jami'an DSS suka ga bukatar kai dauki wajen jawo maslaha suna iya kokari kuma ya yaba musu a kan hakan.

Tinubu ya yi magana kan tallafin man fetur

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur da ya yi.

Bola Tinubu ya ce nan gaba kadan yan Najeriya za su samu sauƙin rayuwa idan tattalin arzikin kasar ya haɓaka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng