Kwamitin Tinubu Ya Waiwayi Masu Kudi, Ana Shirin Laftawa Attajirai Haraji

Kwamitin Tinubu Ya Waiwayi Masu Kudi, Ana Shirin Laftawa Attajirai Haraji

  • Kwamitin gwamnatin tarayya ta bijiro da bukatar a kara karbar 25% a matsayin haraji daga masu kudi a kasar nan
  • Idan an samu yadda ake so, za a karbi 25% din ne daga hannun duk wanda ya ke samun sama da Naira miliyan 1.5 a wata
  • Shugaban kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da garanbawul ga harkokin haraji, Taiwo Oyedele ne ya bayyana shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da garanbawul ga harkokin haraji ya nemi a kara harajin da ake karba daga masu kudin kasar nan.

Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa za a rika karbar harajin ne daga masu samun sama da N1.5m duk wata.

Kara karanta wannan

Ana kokarin shawo kan tsadar fetur, farashin gas din girki ya lula sama

Tinubu
Kwamitin gwamnati na neman a fara karbar haraji daga masu kudi Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

The Cable ta tattaro cewa shugaban kwamitin ya bayyana cewa an dade ana tatsar haraji daga mutanen da bai dace a karbi kudi mai yawa a hannunsu ba, saboda haka ake son bijiro da sabon tsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haraji: Nawa za a karba daga masu kudi

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta ce za a fara karbar 25% daga duk wanda ya ke samun sama da N1.5m duk wata.

Ana sa ran fara karbar harajin da zarar majalisar kasar nan ta amince da kudurin da aka aike mata kan karin kudin.

An gano dalilin rashin biyan haraji

Kwamitin gwamnatin tarayya kan tsare-tsare da haraji ya gano dalilin da ya sa yan kasar da sauran yan kasuwa ba sa biyan kudin haraji yadda ya dace.

Binciken da aka yi ya gano cewa 17% daga cikin 30% na wadanda ke kasuwanci a kasar nan ba sa biyan haraji saboda ba su yarda da gwamnati ba.

Kara karanta wannan

'Akwai matsala': Yadda malami 1 ke koyar da daruruwan dalibai a makarantun gwamnati

Gwamnati na son a kara harajin VAT

A baya mun wallafa cewa kwamitin da Bola Ahmed Tinubu ya kafa kan tsare-tsare da yi wa haraji garanbawul na duba yadda za a kara VAT da ake karba daga yan kasar nan.

Ana son a kara VAT na kayan da ake saye ko sayarwa kuma kwamitin ya nemi da a kara kason kudin da ake ba kananan hukumomi da jihohi zuwa 90% tare da ba gwamnatin tarayya 10%.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.