Tinubu Ya Sake Magana kan Tallafin Mai, Ya yi Albishirin Samun Sauki

Tinubu Ya Sake Magana kan Tallafin Mai, Ya yi Albishirin Samun Sauki

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce duk wahalhalun da ake fama da su a Najeriya ba abin da ya kamata a tayar da hankali ba ne
  • Shugaban kasar ya bayyana cewa duba da matakan da suke dauka akwai haske a gaba kuma yan Najeriya za su yi farin ciki
  • Bola Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur da wasu tsare tsaren cigaba da gwamnatinsa ta kawo a tarayyar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan tsare tsaren gwamnatinsa musamman cire tallafin man fetur.

Bola Ahmed Tinubu ya ce dukkan matsalolin da mutane suke gani sun addabi Najeriya, za a iya magance su.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Tinubu ya tafi Faransa,' gwamnati ta yi wa masu adawa martani

Bola Tinubu
Tinubu ya yi albishir din samun sauki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya wakilci Bola Tinubu yayin wani taro a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi magana kan tallafin mai

Bola Tinubu ya ce daga cikin manyan matakan da ya dauka akwai cire tallafin man fetur da dabarun magance bashin Najeriya.

Bola Tinubu ya ce yan Najeriya su kwantar da hankalinsu a kan wahalar da ake fama da ita musamman kan cire tallafin man fetur.

Tinubu ya yi bushara da cewa nan gaba kadan Najeriya za ta ci galaba a kan matsalolin kuma kasar za ta zama mai karfin tattali fiye da yadda take a baya.

Yadda aka ruguza tattalin Najeriya

Peoples Gazette ta ce Bola Tinubu ya ce daga cikin abubuwan da suka mayar da tattalin Najeriya baya akwai yawan dogaro da albarkatun man fetur.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi lokacin fita a kangi, ya kawo hanyoyin magance matsaloli

Shugaban kasar ya ce lamarin ya jawo rashin samar da wadatattun sana'o'i ga matasa musamman lura da yadda ake kara yawa a Najeriya.

Bola Tinubu ya yi albishir da cewa a yanzu haka akwai tsare tsaren da yake kokarin kawowa a kan kudi da tattali da za su kara bunkasa Najeriya.

Magana kan takarar Tinubu da Atiku a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Dele Momodu ya bukaci masu neman hana Atiku Abubakar takara a zaɓen shekarar 2027 su fara tunkarar Bola Ahmed Tinubu.

Dele Momodu ya bayyana cewa matukar Atiku Abubakar yana cikin koshin lafiya bai ga abin da zai hana shi tsayawa takara ba sai dai mutane suna da yancin kin zabensa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng