Gwamna a Arewa Ya Zabtare 55% a Farashin Shinkafa da Wasu Kayan Abinci

Gwamna a Arewa Ya Zabtare 55% a Farashin Shinkafa da Wasu Kayan Abinci

  • A kokarin tallafawa al'umma saboda halin ƙuncin da ake ciki, gwamnatin Sakkwato ta sayo kayan abinci na N14bn
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya sanar da rage kaso 55% na farashin shinkafa da wasu kayan masarufi, ya kafa kwamitin da zai sa ido
  • Ya kuma tabbatar da gwamnatinsa za ta ci gaba da wannan aiki daga nan zuwa lokacin da za a samu sauki daga tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya karya farashin shinkafa da wasu kayan masarufi da gwamnatinsa ta sayo domin sauƙaƙawa al'umma.

Gwamna Aliyu ya rage kaso 55% na farashin buhun shinkafa da wasu kayan abincin da aka sayo domin ragewa al'umma raɗaɗin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamnatin Sakkwato ta karya farashin shinkafa da wasu kayan masarufi Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya sanar da haka ne a wurin kaddamar da kwamitin da zai sa ido kan aikin ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karya farashin abinci a Sokoto

Ya ce wannan mataki na sayo kayan abinci da sayarwa mutane a farashi mai sauki zai taimaka wajen rage zafin cire tallafin man fetur a ƙasar nan.

Gwamma Aliyu ya kara da cewa kowane magidanci na da damar zuwa ya sayi waɗannan kayan abinci a faɗin gundumomi 244 na jihar Sakkwato.

Da yake jawabi ga ƴan kwamitin, Ahmed Aliyu ya ce:

"Ku kaucewa nuna wariyar siyasa, ƙabila ko addini yayin sauke nauyin da muka ɗora maku, ku tabbata kowane magidanci ya samu domin saboda su aka sayo waɗannan kayan abinci."

Gwamna Aliyu ya buƙaci taimakon masu kudi

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da wannan aiki na sayar da abinci a farashi mai sauƙi har zuwa lokacin da za a samu sauƙi a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi lokacin fita a kangi, ya kawo hanyoyin magance matsaloli

Ya yi kira ga masu hannu da shuni da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa hannu da gwamnati wajen inganta rayuwar al'umma.

Ahmed Aliyu ya buƙaci malamai su jawo hankalin mabiyansu kan muhimmancin taimakawa juna, rahoton Punch.

Gwamnatin Sokoto ta fara binciken Tambuwal

Ku na da labarin gwamnatin Sokoto ta waiwayi tsohon gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, za ta fara bincikensa kan zargin karkatar da N16.1bn.

Kwamitin shari'ar da aka dorawa alhakin binciken gwamnatin Tambuwal ya ce zai gano inda aka kai kudin hannayen jarin jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262