Shari'ar N1.6bn Za Ta Zo Karshe, EFCC da Tsohon Akanta Janar Za Su Daidaita
- Ana dab da kawo karshen shari'ar da gwamnatin tarayya ke yi da tsohon Akanta janar, Anamekwe Nwabuoku kan almundahana
- Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta zargi tsohon Akanta da karin wani mutum da wawashe kudin kasa
- Yanzu haka an fara tattaunawa kan batun da zimmar, bayan an cimma matsaya tsakanin 'yan EFCC da Anamekwe Nwabuoku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Tsohon Akanta Janar na Najeriya, Anamekwe Nwabuoku ya shiga yarjeniniya domin kawo karshen shari'ar da hukumar EFCC ke yi da shi a kotun kasar nan.
Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta shigar da tsohon Akanta janar na riko, Anamekwe Nwabuoku gaban kotu kan zargin badakalar Naira biliyan 1.6.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a zaman da aka yi a babbar kotun tarayya da ke Abuja, lauyan EFCC, Ogechi Ujam ta ce an cimma yarjejeniya da Anamekwe Nwabuoku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cimma matsaya da EFCC kan binciken N1.6bn
Jaridar Ripples ta wallafa cewa tsohon Akanta janar na riko a kasar nan, Anamekwe Nwabuoku da hukumar EFCC sun cimma matsaya kan shari'ar zargin almundahana.
Duk da hukumar EFCC ba ta bayyana wa kotu sauran batutuwan da yarjejeniyar ta kunsa ba, amma ta shaidawa Mai Shari'a James Omotosho cewa an samu fahimtar juna.
Ana duba yarjejeniya kan 'badakalar' tsohon Akanta Janar
Lauyan EFCC, Ogechi Ujam ta shaida wa kotu cewa Mista Nwabuoku da Felix Nweke da ake tuhuma da almundahana sun rubuto wata yarjeniniya kan lamarin.
Ta bayyana cewa yanzu haka sun mika takardar ga shugaban hukumar EFCC, Ola Olukayede domin a nazarci batun, kuma an dage zaman zuwa 2 Disamba, 2024 domin amincewa da yarjejeniyar.
Kotu ta sammaci tsohon gwamna kan almundahana
A baya mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da sammacin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da ya bayyana a gabanta kan zargin almundahanar N110bn.
Sammacin babbar kotu ya biyo bayan wasan buya tsakanin hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'anniti (EFCC) da tsohon gwamnan da ya ke kin halartar zaman kotu kan zargin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng