An Rasa Rayuka yayin da Wasu Tireloli Suka Murkushe Masu Keke Napep

An Rasa Rayuka yayin da Wasu Tireloli Suka Murkushe Masu Keke Napep

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota da sanyin safiyar ranar Litinin, 14 ga watan Oktoban 2024 a jihar Oyo
  • Hatsarin motan ya ritsa da wasu ababen hawa guda huɗu da suka haɗa da tireloli biyu da keke Napep guda biyu
  • Mutum shida ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da wasu mutum buyar kuma suka samu raunuka sakamakon aukuwar hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Oyo - Aƙalla mutane shida ne aka tabbatar da rasuwarsu yayin da wasu mutum biyar suka jikkata a wani hatsarin da mota ya auku a jihar Oyo.

Hatsarin motan ya auku ne a kan hanyar Akanran a yankin Ona Ara a ƙaramar hukumar Ibadan da sanyin safiyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da wani gini mai hawa 2 ya rufta, bidiyo ya bayyana

Hatsarin mota ya auku a Oyo
Mutum shida sun rasu a hatsarin mota a jihar Oyo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Hatsarin mota ya auku a jihar Oyo

Jaridar The Nation ta rahoto cewa hatsarin ya auku a tsakanin wasu tireloli guda biyu da Keke Napep guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin waɗanda suka jikkata har da wani yaro da mahaifiyarsa ta rasu a mummunan hatsarin da ya auku.

Mutum biyar da suka samu raunukan sun haɗa da wasu ƴan makarantar firamare guda biyu, inda aka kai su asibitin Amuloko da ke kusa da wajen, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Yadda hatsarin ya auku" - Jami'i

Wani ma'aikacin hukumar kula da sufuri ta jihar Oyo (OYRTMA) wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne sakamakon lalacewar birkin ɗaya daga cikin tirelolin.

"Bayan ta ƙwace sai ta danne wata Keke Napep guda ɗaya. Ɗaya tirelar wacce ke tahowa a bayanta, a ƙoƙarin kauce mata sai ta danne wata keke Napep."

Kara karanta wannan

IGP ya tuna da iyalan 'yan sandan Kano da suka rasu a hatsarin mota

"Mun fahimci cewa mutane shida sun rasu yayin da wasu mutane biyar suka samu raunuka. Dukkaninsu an garzaya da su zuwa asibiti."

- Wani ma'aikacin OYRTMA

Ɗan tsohon gwamna ya rasu a hatsarin mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da rasuwar Faisal, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi.

Faisal Ahmed Mohammed Makarfi ya rasu ne a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a hanyar Kaduna zuwa Zaria a ranar Asabar, 12 ga watan Oktoban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng