Cire Tallafi: Shugaban NNPCL Ya Bayyana Tagomashin da Najeriya Ta Samu

Cire Tallafi: Shugaban NNPCL Ya Bayyana Tagomashin da Najeriya Ta Samu

  • Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari ya yi ƙarin haske kan cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi
  • Mele Kyari ya bayyana cewa cire tallafin ya sanya an daina fasa ƙwaurin man fetur zuwa ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya
  • Ya nuna a baya da akwai tallafin mai, masu fasa ƙwauri na samun riba sosai idan suka fitar da man fetur zuwa ƙasashen makwabta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana amfanin cire tallafin man fetur.

Mele Kyari ya bayyana cewa cire tallafin mai a Najeriya ya yi matukar rage fasa ƙwaurin man fetur da ake yi a iyakokin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Soke hukumar EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa, ya ba da shawara

Mele Kyari ya magantu kan cire tallafin mai
Mele Kyari ya ce cire tallafi ya hana fasa kwaurin man fetur Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

Mele Kyari ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels tv a ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Amfanin cire tallafin mai", Mele Kyari

Shugaban kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa tallafin ya haifar da rashin daidaiton farashi a tsakanin Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita, lamarin da ya sa ake samun riba daga yin fasa ƙwaurin.

The Punch da ta bibiyi hirar ta ce Mele Kyari ya nuna cewa kafin a cire tallafin mai, bambancin da ke tsakanin farashin fetur da ƙasashe makwabta na da girma, wanda hakan ya sa masu fasa ƙwauri ke cin karensu babu babbaka.

"Cire tallafi ya daidaita farashin man fetur, wanda hakan ya kawar da ribar da ake samu daga fasa ƙwauri"
"Cire tallafin man fetur a Najeriya ya kawo sauyi a yaƙin da ake yi da fasa ƙwauri a kan iyakokin ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnan Zamfara ya fadi halin da ake ciki

"Shekaru da dama, tallafin ya samar da dama ga masu fasa ƙwauri domin samun riba daga bambancin farashin da ke tsakanin Najeriya da ƙasashe makwabta."

- Mele Kyari

Ƴan kasuwa sun hurowa NNPCL wuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN) ta kunnowa kamfanin man Najeriya (NNPCL) wuta awanni bayan ya kara kudin da yake sayar masu da fetur.

Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Shettima ya bukaci NNPC da ya sayar wa ƴan ƙungiyarsu man fetur a farashin da matatar Dangote ke bayarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng