Dara Ta Ci Gida: Yan Ta'adda Sun Aika Kasurgurmin Dan Bindiga Kachalla Lahira

Dara Ta Ci Gida: Yan Ta'adda Sun Aika Kasurgurmin Dan Bindiga Kachalla Lahira

  • Karshen rikakken dan ta'adda, Kachalla Ibrahim Gurgun Daji ya zo a hannun wasu yan bindigar da aka yi arangama
  • An gano gawar Kachalla a yashe ranar Lahadi, wanda kafin mutuwarsa ya takurawa jama'a da satar bayin Allah
  • Haka kuma Kachalla ya shahara wajen ba wasu miyagun yan ta'addan da ake nema mafaka a wani kauye a Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara - Rikici ya balle tsakanin dabar Gurgun Daji da wata dabar daban, wanda ya jawo hallaka daya daga cikin jagororin yan ta'adda da su ka addabi mazauna Zamfara da kewaye.

Rahotanni sun bayyana cewa an tarfa jagoran yan ta'adda Kachalla Ibrahim Gurgun Daji, a Kwanar Nasiru da ke Mada a karamar hukumar Gusau.

Kara karanta wannan

'Ta kone kurmus,' Matashi ya babbaka kakarsa mai shekaru 60 da fetur

Zamfara
An kashe dan ta'adda a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Zagazola ta tattaro cewa wata dabar yan ta'adda ta kashe Kachalla Ibrahim Gurgun a ranar Lahadi bayan kazamar arangama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Kachalla ya addabi mazauna Zamfara

An zargi jagoran yan ta'adda Ibrahim Gurgun Daji da gallazawa matafiya da sauran mazauna hanyar Kwatarkwashi-Mada da kewaye.

An gano cewa ya kitsa miyagun ayyukansa ne daga kauyen Shangel da ke kauyen Mada, inda ya gawurta wajen satar mutane har cikin garin Gusau.

Yadda Kachalla Gurgun Daji ya boye yan bindiga

An gano yadda dan ta'adda, Kachalla Ibrahim Gurgun Daji ya rika ba sauran miyagun yan ta'adda da sauran bata-garin jama'a mafaka ciki har da Bello Taggoje.

Kisan Kachalla Ibrahim Gurgun Daji zai kara bunkasa yakin da sojojin yan kasar nan ke yi da yaki da ta'addanci a fadin kasar nan.

Gwamnati za ta yi maganin yan ta'adda

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya fadi abin da zai faru ga masu ba yan ta'adda bayanai

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Zamfara ta ce ana kokarin magance matsalar tsaro da ta addabi mazauna jihar da kewaye domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi.

A lokacin da ya ke bayani kan halin da rashin tsaro ke ciki a jihar, gwamna Dauda Lawal Dare ya jaddada cewa duk da kokarin da su ke yi, amma harkar tsaron na hannun Allah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.