An Kona Gidan Mai Unguwa da Ofishin Yan Sanda kan Garkuwa da Mutane

An Kona Gidan Mai Unguwa da Ofishin Yan Sanda kan Garkuwa da Mutane

  • An samu barkewar mummunar rikici kan zargin garkuwa da mutane da wasu matasa suka yi a karamar hukumar Etsako ta jihar Edo
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu matasa ne da suke zargin ana garkuwa da yan uwansa suka tunkari ofishin yan sanda, suka kona shi
  • Lamarin ya faru ne bayan an tono gawar wani matashi da ake zargin an yi garkuwa da shi, aka birne shi a wani gida da ke Etsako

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - An samu barkewar mummunan rikici a Edo wanda ya jawo asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.

Rahotanni na nuni da cewa wasu matasa a jihar sun dauki doka a hannu bisa zargin garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

An ceto mutane wajen yan bindigar da suka ƙona dan sanda a kasuwa

Jihar Edo
Matasa sun kashe rayuka da kona ofishin yan sanda a Edo. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Etsako ta Gabas ta jihar Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa sun kashe mutane a Edo

An ruwaito cewa matasa a jihar Edo sun kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane sun mika shi ga yan sanda.

Bayan mika matashin, sun kwato shi daga baya kuma suka bukaci ya nuna musu gidan shugaban yankin inda suka samo gawar wani da aka yi garkuwa da shi da wasu kasusuwa da aka birne.

Daga nan suka fara kone kone har suka kona gidan shugaban Fulanin unguwar, suka lalata wuraren sana'a da galibi na Hausawa ne kuma aka kashe wasu mutane da dama.

Matasa sun kona ofishin yan sanda

Daga gidan shugaban unguwar matasan suka nufi ofishin yan sandan yankin suka cinna masa wuta ya kone kurmus.

Kara karanta wannan

Hankali ya tashi yayin da wata mata da jikokinta 4 suka bakunci lahira daga shan koko

Punch ta ruwaito cewa fusattatun matasan sun kona kayayyakin ofishin yan sandan har da motocin da ake aikin sintiri da su.

Kwamishinan yan sanda da wasu manyan jami'ai sun ziyarci wajen da abin ya faru kuma sun yi alƙawarin yin bayani da zarar an tattara bayanai.

Sojoji sun hallaka yan ta'adda a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan yan ta'adda masu garkuwa da mutane a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

An kama manyan yan ta'adda uku da ake zargin sun dauki shekaru suna mummunan ta'addanci tsakanin jihohin Taraba da Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng