‘Allah Bai Halicci Dan Najeriya domin Shan Wahala ba,’ Obasanjo Ya Dura kan Shugabanni
- Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan halin wahalar rayuwa da talakawa ke ciki a fadin Najeriya
- Cif Olusegun Obasanjo ya dura kan shugabanni yana mai cewa Allah ya samar da abubuwan da za a saka talaka ya ji dadin rayuwa
- Tsohon shugaban kasar ya bayyana rawar da dukkan yan Najeriya za su taka wajen ganin an ceto kasar nan daga halin da take ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci a kawo karshen matsalolin Najeriya da suka addabi al'umma.
Obasanjo ya yi magana ne yayin wani taron cocin Methodist a Abuja na cika murnar shekaru 40 da kafuwa.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya wakilci shugaba Bola Tinubu a taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Bai kamata talaka ya sha wahala ba' - Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce matsalolin Najeriya sanadiyyar mummunan shugabanci ne.
A karkashin haka, Obasanjo ya ce Allah ya samar da dukkan arzikin da ya kamata a yi amfani da su wajen samar da saukin rayuwa ga yan kasa.
Obasanjo ya bukaci a yi addu'a ga Najeriya
Tribune ta ruwaito cewa Cif Olusegun Obasanjo ya ce yan Najeriya sun ki amfani da dimbin arzikin kasa da Allah ya hore musu.
A karkashin haka ya ce ya kamata kowa ya koma ga Allah domin neman shiriya kan yadda aka lalata arzikin da aka ba Najeriya ko za a kamo hanyar gyara kasar.
Tinubu ya nemi hadin kan yan Methodist
A yayin jawabin ministan Abuja da ya wakilci Tinubu, Wike ya ce shugaban kasa ya taya cocin murnar cika shekaru 40 da kafuwa.
Haka zalika ya yi kira ga shugabannin cocin da su cigaba da ba gwamnati hadin kai wajen magance matsalolin Najeriya kamar yadda suka saba.
Obasanjo ya yi magana kan tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasar nan, Cif Olusegun Obasanjo ya dora alhakin ta'addanci kan rashin ilimi.
Cif Olusegun Obasanjo ya koka kan yadda aka samu yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makarantar boko a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng