Gwamnan APC Ya Dakatar da Babban Hadiminsa, Ya Bayyana Dalili

Gwamnan APC Ya Dakatar da Babban Hadiminsa, Ya Bayyana Dalili

  • Gwamnan jihar Jigawa ya dakatar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Alhaji Bashir Ado Kazaure
  • Gwamna Umar Namadi ya yi dakatarwar ne bayan Alhaji Bashir ya sanar da cewa ya amince zai biya sabon mafi ƙarancin albashi
  • Gwamnan ya kuma kafa kwamitin da zai gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa aka yi wannan sanarwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya dakatar da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Alhaji Bashir Ado Kazaure.

Dakatarwar da Gwamna Namadi ya yi wa Alhaji Bashir Ado Kazaure za ta fara aiki ne nan take.

Kara karanta wannan

Ta leko ta koma: Gwamna ya musanta amincewa da mafi karancin albashin N70,000

Gwamnan Jigawa ya dakatar da hadiminsa
Gwamna Namadi ya dakatar da hadiminsa Hoto: @aunamadi
Asali: Facebook

Sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim ne ya sanar da hakan a wata sanarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Gwamna Namadi ya dakatar da hadiminsa?

An dakatar da Alhaji Kazaure ne bisa zarginsa da hannu a wani rahoto da wasu kafafen yada labarai suka yaɗa na cewa Gwamna Namadi ya amince da biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a jihar.

Sai dai, daga baya ya musanta cewa gwamnan ya amince da biyan sabon mafi ƙarancin albashin a wani faifan sautin murya da ya aikawa wani gidan rediyo.

Gwamnati za ta yi bincike

Sakataren gwamnatin jihar ya kuma sanar da kafa wani kwamiti na mutum biyar da zai binciki tushe da dalilin da ya sa aka yi sanarwar amincewa da biyan mafi ƙarancin albashin, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

"Gwamnatin jihar Jigawa ta lura da wata sanarwa cike da damuwa da ke yawo a kafafen yaɗa labarai kan cewa mai girma Gwamna Malam Umar A. Namadi, ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi."
"Wannan abin kunya ne domin kwamitin da gwamnati ta kafa ƙarƙashin jagorancin shugaban ma'aikata domin ya ba da shawara kan albashin da ya dace bai kammala aikinsa ba tare da miƙa rahoto."

- Malam Bala Ibrahim

Gwamna biya mafi ƙarancin albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Ondo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba, Lucky Aiyedatiwa, ya amince da biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya amince zai biya ma'aikatan jihar mafi ƙarancin albashi na N73,000 fiye da wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng