Gwamnan APC Ya Shiga Matsala da Ɗan Majalisa Ya Maka Shi a Kotu da Hadimansa 2

Gwamnan APC Ya Shiga Matsala da Ɗan Majalisa Ya Maka Shi a Kotu da Hadimansa 2

  • Gwamnan APC a Arewacin Najeriya ya shiga matsala bayan dan Majalisar Tarayya daga jiharsa ya maka shi a kotu
  • Dan Majalisar Tarayya, Terseer Ugbor ya maka Gwamna Alia Hyacinth da mukarrabansa biyu kan zargin bata masa suna
  • Hon. Ugbor ya shigar da korafin a babbar kotun jihar da ke birnin Makurdi a jihar Benue a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Dan Majalisar Tarayya daga jihar Benue ya naka gwamna da mukarrabansa a kotu.

Hon. Terseer Ugbor ya dauki matakin ne kan Gwamna Alia Hyacinth game da zargin bata masa suna.

An maka gwamnan APC a kotu kan zargin bata sunan dan Majalisar Tarayya
Dan Majalisar Tarayya ya kai Gwamna Alia Hyacinth kara a kotu kan zargin bata suna. Hoto: Gov. Alia Hyacinth.
Asali: Twitter

An shigar da gwamnan APC kara kotu

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tsallake gida, ya ba Nijar N16m na gyaran masallaci mai shekaru 200

Punch ta ruwaito cewa dan Majalisar da ke wakiltar Kwande/Ushongo ya bukaci a biya shi diyyar N1bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Ugbor ya shigar da korafin ne a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024 a birnin Makurdi da ke jihar.

Sauran wadanda aka maka a kotun sun hada da sakataren yada labaran gwamnan, Tersoo Kula da wani hadiminsa a bangaren sadarwa, Isaac Uzaan.

Bukatar dan Majalisar a kotu kan gwamna

Ugbor ya roki kotun da ta umarci Gwamna Alia da mukarrabansa su goge abubuwan da suka wallafa kansa a shafukan Facebook.

Dan Majalisar ya kuma bukaci kotun ta tilasta wadanda ake zargin su ba shi hakuri tare da wallafa hakan a manyan jaridu biyar da kuma kafofin sadarwa.

Har ila yau, Hon. Ugbor ya bukaci kotun ta ja kunnen gwamnan da mukarrabansa kan cigaba da bata masa suna.

Kara karanta wannan

Damagum: Kotu ta dakile kwamitin gudanarwar PDP, ta ba da sabon umarni

Hakan ya biyo bayan zargin da mukarraban gwamnan suka yi kan dan Majalisar na karkatar da kayan tallafi na yan gudun hijira.

Gwamna Alia ya rufe kamfanonin Samuel Ortom

Mun baku labarin cewa Gwamnatin jihar Benue ta kulle kamfanin tsohon gwamna, Samuel Ortom kan zargin kin biyan haraji na makudan kudi.

Ana zargin kamfanin mai suna Oracle Business mallakin tsohon gwamna, Ortom da kin biyan harajin makudan kudi har N93.5m.

Sai dai wasu na ganin hakan bita da kullin siyasa ne da ake yi domin kassara harkokin kasuwancin tsohon gwamna, Ortom a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.