Shugaban Kamfanin NNPCL, Kyari Ya Yi Babban Rashi, Kashim Shettima Ya Jajanta

Shugaban Kamfanin NNPCL, Kyari Ya Yi Babban Rashi, Kashim Shettima Ya Jajanta

  • An shiga jimami bayan rasuwar yar shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kyari a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayiyar mai suna Fatima Kyari ta rasu a yau Juma'a tana da shekaru 25 kacal a duniya
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya samu halartar jana'izarta ya yi addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kamfanin mai na NNPCL, Mele Kyari ya gamu da babban rashin ƴarsa matashiya.

An tabbatar Kyari ya rasa yarsa ne mai suna Fatima Kyari a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.

Shugaban NNPCL ya yi rashin yarsa matashiya
Shugaban Kamfanin NNPCL, Kyari ya tafka babban rashin yarsa mai shekaru 25. Hoto: NNPC Limited.
Asali: Getty Images

Mene musabbabin rasuwar Fatima Mele Kyari?

Kara karanta wannan

Atiku ya amince gwamnan Bauchi ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP a 2027?

Punch ta ruwaito cewa ba a bayyana silar rasuwar marashiyar ba mai shekaru 25 kadai a duniya har zuwa wannan lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya tura sakon ta'azziya ga shugaban NNPCL kan wannan babbar rashi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Stanley Nkwocha ya fitar a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.

Shettima wanda ya samu halartar sallar jana'izarta a masallacin Annur da ke Abuja ya yi mata addu'ar samun rahama, cewar Vanguard.

Shettima ya jajantawa iyalan shugaban NNPCL, Kyari

"Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yana jajantawa iyalan shugaban NNPCL, Mele Kyari kan rasuwar yarsa mai suna Fatima Kyari."
"Marigayiyar ya rasu ne tana da shekaru 25 kacal a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024 a Abuja."
"Shettima ya yi addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama da ba iyalanta juriyar wannan rashi da suka yi na matashiya da ke kan ganiyarta."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya sake dagulewa, an nada sabon shugaban jam'iyyar, bayanai sun fito

- Kashim Shettima

Ministar Buhari ta yi babban rashi

Kun ji cewa tsohuwar Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen ta yi babban rashin ɗanta guda daya.

Marigayin mai suna Richard ya rasu ne a jiya Asabar 6 ga watan Oktoban 2024 a wani asibiti da ke birnin Tarayya Abuja.

Mrs Tallen ta rike muƙamin Ministar mata a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kafin sauya gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.