An Kai wa Fulani Makiyaya Hari a Filato, Rayuka Sun Salwanta
- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta yi tir da kisan wasu Fulani makiyaya a lokacin da su ke tsaka da kiwon dabbobinsu
- Da ya ke bayyana sunayen wadanda aka kashe, shugaban kungiyar Babayo Yusuf ya ce har shanu masu tarin yawa aka harba
- Ya ce sun sanar da hukumomin tsaro domin su bi wa Fulanin da aka kashe ba tare da sun aikata laifin komai ba hakkinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau- Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bayyana yadda wasu miyagun mutane su ka kai wa Fulani makiyaya farmaki a Filato.
Shugaban kungiyar, Babayo Yusuf ne ya tabbatar da hare-haren, inda ya ce an kashe wasu Fulani a lokacin da su ke kiwo.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an kashe makiyayan a kananan hukumomi daban-daban, sannan an sace wani bafulatanin da ke kiwon dabbobinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanne makiyaya aka kashe?
Shugaban kungiyar Miyetti Allah a Filato, Babayo Yusuf ya ce wasu miyagun mutane sun kashe Bashiru Iliyasu a kauyen Jol, karamar hukumar Riyom.
Sai kuma mutum na biyu da aka kashe mai suna Yahuza Idris a titin Maikatako da ke karamar hukumar Bokkos.
An fada wa jami'an tsaro kisan makiyaya
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta ce an harbe shanu da yawa a lokacin da wasu bata gari su ka kai harin ta'addancin kan Fulani makiyaya a Filato.
Kungiyar ta ce tuni ta sanar da jami'an tsaron farin kaya na (DSS) da yan sanda da sauran wadanda su ka dace domin a dauki matakin kwato hakkin mutanen.
Gwamna ya goyi bayan Fulani makiyaya
A baya mun ruwaito cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya gargadi manoma kan noma wasu filaye da sauran labi a kananan hukumomi da Fulani ke kiwo a kai.
A cewar Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, an zauna tare da cimma matsaya tsakanin manoma da makiyaya kan daina noma a labin da ake kiwo.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng