Damagum: Kotu Ta Dakile Kwamitin Gudanarwar PDP, Ta ba da Sabon Umarni
- Yayin da rikicin PDP ke kara ƙamari, kotu ta shiga lamarin inda ta dakatar da matakin kwamitin zartarwa
- Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja ta haramta dakatar da Damagum daga mukaminsa na shugaban PDP
- Wannan na zuwa ne bayan tsagin jam'iyyar PDP ta dakatar Umar Damagum a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci bayan dakatar da shugaban PDP, Umar Damagum daga mukaminsa.
Kotun da haramtawa kwamitin zartarwa (NEC) da Majalisar Amintattu (BOT) dakatar da Damagum.
Kotu ta yi hukunci kan dakatar da Damagum
Alkalin kotun, Peter Lifu shi ya ba da wannan umarni a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton Channels TV.
Lifu ya ce Damagum ne zai cigaba da kasancewa a matsayin shugaban PDP har zuwa babban taronta a watan Disambar 2025.
Alkalin ya ba da wannan umarni ne bayan korafin da Sanata Umar El-Gash Maina ya shigar game da dakatar da Damagum.
Ya ce a sashe na 42 da 47 da kuma 67 na dokar PDP, za a iya zaben shugabannin jam'iyyar ne kawai lokacin babban taronta.
Damagum: Yadda aka dakatar da shugaban PDP
Wannan na zuwa ne bayan kwamitin gudanarwa karkashin jagorancin Umar Damagun ya dakatar da wasu jiga-jigan PDP.
Yayin zaman, an dakatar da sakataren yada labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba da mai ba ta shawara kan shari'a, Kamaldeen Ajibade.
Jim kaɗan bayan daukar matakin, tsagin jam'iyyar ya dakatar shugabanta, Umar Damagun da sakatarenta, Sam Anyanwu.
Dan PDP ya yi tsokaci ga Legit Hausa
Wani magoyin bayan PDP a Gombe ya yi magana da Legit Hausa kan matakin da tsagin jam'iyyar ya dauka.
Kwamred Abubakar Aliyu ya ce rikicin PDP zai yi matukar tasiri a babban taron jam'iyyar ta kuma zaben 2027 da ake tunkara.
Jigon PDP ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki su kawo karshen matsalar bayan dakatar da Umar Damagum a muƙaminsa.
Ya ce duk da kotu da hana dakatarwar da aka yiwa Damagum, ya kamata a zauna domin dinke barakar da gaggawa.
Tsagin PDP ya nada sabon shugaban
Mun ba ku labarin cewa rikicin PDP ya sauya salo bayan nadin mukaddashin shugaban jam'iyyar ta kasa a yau Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.
Tsagin jam'iyyar PDP a Najeriya ya nada Ahmed Yayari Mohammed a matsayin mukaddashin shugabanta bayan dakatar da Umar Damagum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng