An Ceto Mutane wajen Yan Bindigar da Suka Ƙona Dan Sanda a Kasuwa

An Ceto Mutane wajen Yan Bindigar da Suka Ƙona Dan Sanda a Kasuwa

  • Rahotanni da suka fito daga jihar Anambra na nuni da cewa rundunar yan sanda ta yi nasarar ceto wasu yan jarida wajen yan bindiga
  • An sace 'yan jaridar ne a hanyarsu ta zuwa filin wasan da Najeriya za ta kara da kasar Libiya daga Legas zuwa jihar Akwa Ibom
  • An ruwaito cewa yan bindigar sun tafka ta'asa a wajen da suka kama mutanen ciki har da kashe wani dan sanda da kona gawarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - Rundunar yan sanda ta samu nasarar ceto wasu daga cikin yan jarida da aka sace a kan hanyar zuwa Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

An kama manyan yan bindiga da suka fitini jihohin Arewa tsawon shekaru

Kakakin yan sandan jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga ne ya fitar da rahoto kan ceto mutanen da aka yi.

Yan sanda
An ceto yan jarida a Anambra. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa har yanzu akwai sauran mutanen da suke hannun masu garkuwa da mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace mutane a Anambra

Punch ta ruwaito cewa a yankin Isseke yan bindiga suka tare motar yan jaridar suka wuce da su cikin jeji.

Bayan kama yan jaridar, yan bindigar sun kama wasu yan sanda biyu inda suka kashe daya suka kona gawarsa a tsakiyar kasuwa.

Yan sanda sun ceto mutane a Anambra

Rundunar yan sanda ta sanar da cewa bayan samun labarin garkuwa da yan jaridar ta hada jami'an tsaro da suka shiga jeji domin ceto su.

SP Tochukwu Ikenga ne ya fitar da sanarwar inda ya ce zuwa yanzu an ceto yan jarida shida yayin da ake ƙoƙarin ƙubutar da sauran.

Kara karanta wannan

Tuban Muzuru: Tubabbun Boko Haram sun tsere da makamai, suna barazanar kai hari

Halin da ake ciki a garin Isseke

Mutanen Isseke sun bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin sojojin Najeriya ke sintiri a cikin garin dauke da makamai.

Rundunar yan sandan jihar Akwa Ibom ta bayyana cewa za ta sanar da al'umma halin da ake ciki da zarar an samu wasu bayanai.

An kama yan bindiga a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa sojoji sun samu nasara kan yan ta'adda masu garkuwa da mutane a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

An kama manyan yan ta'adda uku da ake zargin sun dauki shekaru suna mummunan ta'addanci tsakanin jihohin Taraba da Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng