Sanata Buba da Aka Alakanta da 'Yan Bindiga Zai Fito Takarar Gwamnan Bauchi?

Sanata Buba da Aka Alakanta da 'Yan Bindiga Zai Fito Takarar Gwamnan Bauchi?

  • Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu ya ce nan gaba kadai zai ba da amsa ga kiraye kirayen da ake yi na ya fito takarar gwamna
  • Sanata Shehu Buba ya ce al'ummar Bauchi, kungiyoyin 'yan siyasa da sauransu na ta yin kira a gare shi da ya nemi gwamna a 2027
  • A zantawarmu da wani jagoran matasa daga Alkaleri, Yusuf Sulaiman Bala, ya ba Sanata Buba shawarar ka da ya wahalar da kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Sanata Shehu Buba Umar, wanda a kwanakin baya gwamnatin Bauchi ta zarge shi da daukar nauyin ta'addanci ya yi magana kan shirin siyasarsa a 2027.

Sanatan mai wakiltar Bauchi ta Kudu ya bayyana cewa zai amsa kiran al'ummar Bauchi, kungiyoyin siyasa da ke neman ya fito takarar gwamna a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Akwai matsala': Yadda malami 1 ke koyar da daruruwan dalibai a makarantun gwamnati

Sanata Buba ya yi magana kan fitowa takarar gwamnan jihar Bauchi a 2027
Sanata Buba ya ce nan gaba kadan zai amsa kiraye-kirayen fitowa takarar gwamnan Bauchi. Hoto: @SenBalaMohammed, @Benking443
Asali: Twitter

Sanata Buba zai amsa kiran fitowa takara?

Sanata Buba ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a kauyen Zaranda da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisar dattawan ya shaida wa manema labarai cewa:

"Zan ba da amsa ga wadanda suke kirana da na fito takarar gwamna a zaben 2027 da zarar lokaci ya yi. Mu roki Allah ya tsawaita rayuwarmu zuwa lokacin."

"Lokaci bai yi ba" - Sanata Buba

Sai dai sanatan wanda ke takun-saka da gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammad, ya jaddada cewa lokaci bai yi ba da za a fara tattaunawa kan yakin neman zabe.

Sanata Buba ya kuma nuna cewa duk da cewa yana wakiltar Bauchi ta Kudu ne kadai, amma yana kallon kansa a matsayin mai wakiltar muradun jihar baki daya.

Kara karanta wannan

Likitoci, lauyoyi sun nemi Tinubu ya warware matakin NNPCL da fetur ya kai N1030

Ganin cewa jam'iyyarsa ta APC ta lashe kujerar sanata ne kawai a mazabarsa ya ce zai ba da amsa ga masu neman ya fito takarar gwamnan da zarar lokaci ya yi.

"Kada ya wahalar da kansa" - Fantyz

A zantawarmu da wani jagoran matasa daga jihar Bauchi, Yusuf Sulaiman Bala (Fantyz Guy) ya shawarci Sanata Buba da kada ya wahalar da kansa wajen fitowa takara.

Yusuf Sulaiman ya ce ko makaho ya san cewa Gwamna Bala Mohammed ya shimfida ayyuka a jihar Bauchi wanda ya karawa jam'iyyar PDP daraja a siyasar jihar.

Jagoran matasan ya yi nuni da cewa ko da ace 'Kauran Bauchi' zai gama wa'adinsa, hakan ba yana nufin wata jam'iyya wadda ba PDP ba za ta iya lashe zabe a jihar.

Ga dukkanin wadanda ke sha'awar neman takarar gwamna a wasu jam'iyyun adawa, Fantyz Guy ya ce za su yi asarar kudinsu ne kawai domin al'umma PDP za ta sake zaba.

Kara karanta wannan

"A kasa su ke zaune:" Gwamna ya koma makarantar mata a Kano da kayan aiki

MURIC ta kare Sanata Buba

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta kare Sanata Shehu Buba Umar kan zargin daukar nauyin 'yan bindiga.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya ce babu wasu hujjoji da aka gabatar da suka tabbatar da alakar sanatan da 'yan bindiga, ya ce 'siyasa ce kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.