Kwana 1 da Kara Kudin Mai, Gwamnan APC Zai Biya Albashin N70,000, Ya Fadi Lokaci
- A karshe, Gwamnan Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da fara biyan mafi karancin albashi N70,000 a Oktoban nan
- Gwamnan ya sanar da haka ne a yau Alhamis 10 ga watan Oktoban 2024 bayan a baya ya ce ba zai iya biyan karin kudin ba
- Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kamitin sabon albashin, Dakta Manasseh Daniel Jatau ya tabbatar da haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe - Gwamnatin Gombe ta amince da fara biyan mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikatan jihar da na kananan hukumomi.
Kwamitin biyan sabon albashin karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Dakta Manasseh Daniel Jatau shi ya tabbatar da haka.
Gwamnan Gombe ya shirya biyan albashin N70,000
Hadimin gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya a bangaren sadarwa na zamani, Yusuf Alyusra ya wallafa faifan bidiyon Dakta Jatau a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke jawabi ga yan jaridu, Jatau ya ce sun samu tsare-tsaren biyan albashin daga Gwamnatin Tarayya.
Dakta Jatau ya ce kwamishinan kudi, Gambo Magaji zai jagoranci kwamitin duba yawan kudin albashin da za a biya a jihar cikin awanni 72.
An sake kafa kwamiti kan biyan albashi
"Mun yi duba kan abubuwan da muke da su a yanzu da wadanda babu, ina mai tabbatar muku gwamna ya shirya biyan albashin N70,000 a wannan wata."
"Mun tattauna kan haka, mun ba kwamiti na musamman awanni 72 domin kawo rahoto kan lamarin."
Ina mai tabbatar muku a cikin awanni 72 za su dawo da rahoto zuwa ranar Litinin zan tabbatar muku da abin da na fada."
- Manasseh Daniel Jatau
Ma'aikata sun yi maraba da karin albashi
Legit Hausa ta yi magana da wani ma'aikataci a gwamnatin jihar Gombe kan wannan sanarwa.
Abdulkadir Umar ya yaba da matakin gwamnan kan shirin fara biyan albashin N70,000 ga ma'aikatan jihar da kananan hukumomi.
Abdulkadir ya ce suna fatan hakan ya tabbata saboda halin kunci da ake ciki a yanzu a fadin kasa baki daya.
'Ba zan iya ba": Gwamna kan albashin N70,000
A baya, kun ji cewa Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ce ba zai iya biyan ma'aikatan jiharsa sabon mafi karancin albashin N70,000 ba.
Gwamnan ya yi nuni da cewa ko tsohon albashin N30,000 sai jihar ta yi da kyar ake iya biya sakamakon matsin tattalin arziki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng